An kai farmaki dajin Pasali da Kuje inda aka rushe maboyar yan ta’adda.

0
136

A yau Laraba ne jami’an hukumar babban birnin tarayya Abuja suka kai samame  a wani dajin Pasali da ke kan hanyar Kuje zuwa Gwagwalada da ake zargin maboyar ‘yan ta’adda ne.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci g aba da gudanar da aikin rusau a Kuje a rana ta uku domin inganta matsalar tsaro.

Babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da tilastawa ministar babban birnin tarayya Abuja, Ikharo Attah bayan an kammala atisayen, ya ce rusa dajin Pasali da ke kusa da sakatariyar hukumar ilimi ta karamar hukumar Kuje, an yi shi ne domin a kawar da haramtattun abubuwa da kuma dawo da tsarin da da gwamnati ta amince da shi.

“Ministan babban birnin tarayya Abuja da kwamishinan ‘yan sanda suna da cikakkiyar masaniya game da atisayen, kuma za mu ci gaba da kwato yankunan da aka ware domin wasu ayyuka na musamman.”

A cewar sarakunan yankin ,matsayinsu na masu rike da sarautar gargajiya, bai kamata su ba su damar saye da gina layin dogo na Kuje ba, kuma a wasu wuraren da ake zargin sun sabawa doka.

Mutanen da abin ya shafa sun zargi sarakunan da rashin yin abin da ya dace don kare sha’awarsu amma sun cutar da su.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa Briget Ekelechukwu, Divine Choosen Spiritual Ministry Less Privileged ta ce: “Mun shafe sama da shekaru 12 muna nan, na san yankin nan layin dogo ne amma sarakuna da jama’arsu sun yaudare ni cewa hanyar jirgin kasa ba ta zuwa nan.

“Na gano hanyar jirgin kasa ne kimanin shekaru 5 da suka wuce, ina da yara kusan 19, na yi rajista a ma’aikatar amma ban kammala rajistar gidan marayu ba, rajista na da sakatariyar ci gaban jama’a .

Wani da abin ya shafa, Benedict Chidozie ya yi nadama cewa, “ta yaya mutane za su zo su yi gini ba tare da amincewar sarkin gargajiya ko danginsa ba? Su ne musabbabin matsalarmu.”

Sai dai sakataren Gomo na Kuje, Alhaji Mohammed Usman ya musanta zargin da ake yi wa sarkin  ya kuma bayyana shi a matsayin karya.

Ya ce: “Abin da mutane ke fada karya ne, su kawo yarjejeniyar da mai martaba ya sayar musu da fili, duk wanda ke zargin Gomo ya kawo hujja, ba mu da wani abin boyewa.”

Ga David Musa, rushewar zai kawo wa yankin zaman lafiya  ya kasance maboyar masu laifi ne saboda bishiyoyib da sauran abubuwa.

“Wadanda ake zargin ‘yan fashi suna zuwa nan ne domin su huta da rana sanan su shiga aiki da dare, kamar jiya an yi garkuwa da mutane kusan 15 a unguwar Kwaku da ke Kuje.

Fatima Abubakar