An samu hastarin tarwatsewan danyen mai, ya kashe mutane da dama a jihar Ribas

0
42

 

Ana fargabar mutane da dama da suka hada da mata sun mutu sakamakon hatsarin tarwatsewan danyan mai a wani wurin hako danyen mai a unguwar Rumuekpe da ke karamar hukumar Emuoha a jihar Ribas.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na safiyar ranar Juma’a inda daya daga cikin motocin bas dauke da danyen mai ya kama da wuta a lokacin da yake kokarin tafiya zuwa wani haramtacciyar wurin tace mai a yankin.

Wani masanin muhalli kuma babban darakta Youths and Environmental Advocacy Centre, Fyneface Dumnamene ya tabbatar da faruwar lamarin. inda ya ce sunvsamu labarin faruwar lamarin ne ta hanyar ‘tsarin mayar da martani ga malalar danyen mai.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar wa afkuwar lamarin, inda ta ce, “Tuni jami’in ‘yan sanda na yankin ya isa wurin.”

Daga:Firdausi Musa Dantsoho