An share inda ake zaton maboyar yan ta’adda ne a Mabushi.

0
44

’Hukumar babban birnin tarayya, FCTA, a yau Laraba ta gargadi ’yan asalin birnin tarayya Abuja, su daina ba da hayar itatuwan tattalin arzikinsu ga ’yan sara-suka da babanbola .

Babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da tabbatarwa da Ministan babban birnin tarayya, Ikharo Attah, ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci aikin tsaftace muhalli a Mabushi da Jahi a Abuja.

Ya koka da cewa, ba za a amince da masu mallakar fili ko gine-ginen da ba a gina su ba su yi hayar kadarorinsu don yin amfani da fili ba bisa ka’ida ba sabanin yadda aka tsara a cikin tsarin.

Ya kara da cewa daga yanzu gwamnati za ta kai karar wanda ya mallaki kadarorin ga ‘yan sanda kuma idan laifin ya yi yawa ‘za mu kai rahoto ga Ministan domin daukar matakin da ya dace’.

A cewarsa, “A cewar sa,za mu  cire duk wani bacha na babanbola, da shanties da ke  unguwar Mabushi kusa da gidan Orji Uzor Kalu.

kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Sunday Babaji, ya bukaci ministan babban birnin tarayya, Muhammad Bello, da ya tabbatar da cewa an share wannan wuri domin yin hakan a wannan yankin zai inganta tsaro.

Yayin gudanar da sharan an gano katin shaidar dan kasa da fasfo na kasa da kasa, wanda watakila an sace shi, wannan yanki ne babba kuma ba zai dace babanbolas su tsaya a nan ba. Mun mika su ga hukumomin da suka dace don gano masu katin shaida da fasfo na kasashen waje.

“Mun kuma ga kayan kwastan, mun ga hular ‘yan sanda, rigar makamai na hukuma wacce za ta iya zama na wata hukuma ta gwamnati.”

Ya koka da yadda a yanzu noman cashew ya zama maboyar ’yan ta’adda a Abuja, “Bishiyar cashew ba bishiyar tattalin arziki ba ce  sun zama mafakar masu aikata laifuka. .

Don haka ya yi gargadin cewa, “Idan wani ya bayar da hayar dukiyarsa ga wadanda suka shiga ba bisa ka’ida ba, , kuma idan muka samu mai shi, za mu kai karan shi  ga ’yan sanda.

Mataimakin daraktan da ke kula da kare muhalli a Abuja, AEPB, Kaka Bello, yayin da yake magana a madadin Daraktan AEPB Osilamah Braimoh, ya ce babu gudu babu ja da baya a kan shawarar cewa duk masu sayar da kayan , babanbolas, su koma jibge wuraren da za su yi kasuwancinsu. .

Ya kara da cewa ba abin yarda ba ne a ce ana amfani da wuraren zama kuma ya zama wurin tarin sharar gida .

“Abun da ke tattare da muhalli yana lalata muhalli da kuma yin illa ga lafiyar al’ummar yankin.

“Duk wanda ke son yin sana’ar gyaran shara, to ya yi ta a wuraren da ake zubar da shara a Abuja. . “Mun yi tarin tarurruka da su, inda muka shaida masu cewa idan har za su yi aiki, to dole ne su yi amfani da wurin da ake zubar da shara kuma muna da fili fiye da  90 da za su iya amfani da su wajen kasuwancin su

Daga Fatima Abubakar