FITATTUN ABINCIN GARGAJIYA GUDA GOMA DA YADDA AKE SARRAFASU

0
1665

  1. Tuwon masara = masara abinci ne na hausawa wanda akan iya sarrafa ta, ta hanyan daban daban. Zaa samu masara da ruwa, da farko zaki saka ruwa a tukunya ki daura kan wuta idan ya tafasa sai kiyi talgen ki, kisa kanwa kadan idan talgen ya nuna sai ki tuka tuwon ki watau ki rinka saka garin masaran kadan kadan kina tukawa, idan yayi miki kaurin da kikeso sai ki rufe tukunyan ki barshi ya nuna, sai ki kara saka muciyan ki, ki tuka shi sannan ki kwashe kiyi malmala idan kinaso.                                           
  2. Tuwon shinkafa = zaki samu shinkafan tuwo da ruwa zaki saka ruwa akan wuta a cikin tukunya, idan ya tafasa sai ki wanke shinkafan tuwan naki ki saka sai ki rufe tukunyan ki idan shinkafan ki ta fara dahuwa ruwan yaja sai ki rage wutan, idan ruwan cikin shinkafan ya gama tsotsewa sai ki tuka shinkafar sannan ki kwashe idan malmala zakiyi sai kiyi.                   
  3. Tuwon dawa = abincin malam bahaushe, ana sarrafa dawa ta hanya daban daban tana da sinadarai daban daban. Zaki samu nikakken garin dawa,kanwa da ruwa. Ki daura ruwa akan wuta idan ya tafasa, bayan kin tankade garin dawar ki sai ki dibi kadan kisa a ruwa ki dama shi sai kiyi talgen ki, kina zubawa a cikin ruwan zafin kina juyawa haka zakita juya shi kar yayi gudaje, sai ki barshi ya dahu sai kisa garin dawan ki kadan kadan kina tukawa zakiga wani yauki yakeyi idan yayi yanda kikeso barshi ya kara nuna sai ki kwashe.                                                                         
  4. Sakwara = abinci ne daya samu asali daga doya, yana daga cikin abuncin dake gina jiki kuma ta karawa jiki kuzari. Zaki samu doyan ki, ki fer ki yankashi da girma sai kisa a kukunya da ruwa idan doyan ya nuna, sai ki samu turmi mai kyau ki wanke sosai, sannan ki rinka zuba doyan ki kina dakawa sai ki saka ruwan doyan kadan kina dakawa dan ya hadu da kyau, idan ya hadu yanda kikeso sai ki kwashe.                       
  5. Danbun shinkafa = zaa samu shinkafa, zogale, albasa, mai, attarugu, gyada, maggi da gishiri. Zaki samu shinkafar ki, ki barza sai ki wanke ki samu tukunyan yin danbu watau tukunya mai huji, sai kid aura akan tukunya da ruwa a ciki idan shinkafan ya tiruru sai ki sauke ki hada dukkan kayan hadin a ciki, sannan ki maida akan wuta idan ya nuna sai ki sauke ya nuna.                                                                                           
  6. Waina = zaki samu danyen shinkafa ki wanke sai ki nika kisa yeast, baking powder, sugar da gishiri kadan,ki bari ya tashi idan ya tashi sai ki samu tandan ki kina saka mai ki dibi kullun kina sawa daidai girman da kikeso, idan yayi sai ki juya dayan gefen shima yayi sai ki kwashe.                                                                                                 
  7. Gurasan tanderu = zaki samu fulawa, yis, kantu/ridi, sikari da gishiri. Ki samu flawar ki, ki tankade sai kisa yis, kisa ruwa ki kwaba kada kwabin yayi ruwa yayi dan tauri idan kina son gurasa mai sikari, sai ki zuba sikari a cikin kwabin, idan mai gishiri kikeso sai ki zuba gishiri a cikin kwabin sai ki bari yayi awa uku zuwa hudu zakiga ya tashi, amma idan lokacin sanyine sai kiyi kwabin ki da daddare da safe sai kiyi gurasar ki.

Ki zuba karare a cikin tanderu, ki kunna wuta domin yayi zafi idantanderun yayi zafi kuma karan ya cinye sai ki yayyafa ruwan kanwa a ciki, ki saka tsintsiya ki share tokar data makale a cikin tanderun. Sannan ki kawo kwabin ki, ki yishi yayi fadi kiyi da hannun ki yanayin fadin da kikeso, idan kinason kanti/ridi sai kisa kadan a kai sai ki saka a cikin tanderun, idan kin gama sai ki kawo tire ki rufe dashi. Ki bari yayi minti ashirin ko talatin zakiji kamshi na tashi sai ki samu wuka da tire kina bambarota da wuka kina sawa a tire.                                                                                                           

  1. Alkubus = zaki samu alkama, fulawa, yis, gishiri, mai da sukari. Zaki tankade garin alkama dana fulawa a hada su waje guda, sai ki zuba yis da sikari da gishiri ki kwaba amma kwabin yafi kwabin fanke tauri. Sai a bari ya tashi sannan a zuba mai kadan a kara buga shi, sannan a dauko gwangwani ana shafa masa mai ana zubawa a ciki ko kuma asa a leda a kulle sannan a turara shi idan ya nuna a sauke.                                       
  2. Dan wake = zaa samu garin alabo, garin dawa, garin wake, kuka, gishiri da kanwa. Sai ki hadesu wuri daya ki kwaba kar yayi ruwa sai kid aura ruwa akan wuta, idan ya tafasa sai ki samu kwabin naki ki rinka gutsurowa yanda kike son girman shi kina jefawa a cikin wutan, idan ya nuna zakiga ruwan yayi kauri sai ki sauke.                             
  3. Sinasir = ki samu shinkafar ki, ki wanke sai ki samu shinkafar kadan ki tapasa sai ki juye a cikin shinkafan da kika wanke sai kisa yeast ki bari ya tashi sannan kisa sikari ki shima zai kara sawa ya tashi sannan ki samu fry pan non-stick, kid aura a wuta sai kisa kullun kin a sinasir din a ciki yanda kike son girman shi, sannan ki rufe da murfi idan yayi ki juya bayan shima yayi sai ki cire.                                                                                                                                                                                            DAGA FAIZA A. GABDO