APC ta fara tantance ‘yan takarar shugaban kasa gabanin zaben fidda gwani

0
98

 


Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara tantance masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Ana gudanar da atisayen ne a asirce a wani shahararren otel dake Abuja, babban birnin tarayya (FCT).

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu; Tuni dai sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore, da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka isa wurin da za a gudanar da atisayen, kamar yadda gidan talabijin in Channels ya tabbatar.

Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma dan majalisa mai wakiltar yankin Ogun ta tsakiya, Sanata Ibikunle Amosun, wanda kuma ke neman tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC na cikin wadanda suka isa wurin da za a gudanar da atisayen.

A halin da ake ciki, wata majiya ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar APC na karkashin jagorancin Mista John Oyegun, tsohon gwamnan jihar Edo ne kuma tsohon shugaban jam’iyyar na kasa.

Fiye da mambobin jam’iyyar 20 da suka hada da ministocin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, da ‘yan kasuwa, da dai sauran su, sun karbi fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da kuma nuna sha’awarsu a kan Naira miliyan 100.

Yayin da masu neman shugabancin kasar suka biya wa kansu kudaden fom a wasu lokuta, kungiyoyi daban-daban sun sayi tikitin tsayawa takara ga wadanda suka fi so – matakin da wasu daga cikin wadanda suka amfana suka yi watsi da shi.

Daga cikin wadanda suka fito fili suka ki amincewa tiketin takarar jam’iyyar APC da aka siya musu sun hada da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma shugaban bankin ci gaban Afirka (AfDB), Dr Akinwumi Adesina.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho