Kotu ta bawa EFCC umarnin tsare Okorocha bisa zargin almundahanar N2.9bn

0
25

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha a hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC har sai an yanke shawarar neman belinsa.

Wadda za’a hada da Okorocha a hannun EFCC, jigo ne a jam’iyyar APC, kuma aminin tsohon gwamna, Anyim Nyerere Chinenye.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya ba da umarnin ne a ranar Litinin bayan da Okorocha, Chinenye da kamfanoni biyar suka gurfana a gaban kuliya bisa zarge zarge 17 na halasta kudaden haram da EFCC ta shigar.

Mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraren karar Okorocha da Chinenye har zuwa ranar Talata.

Kamfanoni biyar sune: Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited da Legend World Concepts Limited.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho