ATIKU DA OBI SUN DAUKAKA KARA GAME DA SAKAMAKON ZABEN SHUGABAN KASA DA AKA GUDANAR A RANAR 25 GA WATAN FABRAIRU.

0
44
Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party da na Labour Party, Atiku Abubakar da Peter Obi sun garzaya kotun zaben shugaban kasa domin neman izinin duba kayan zaben da aka yi amfani da su a zaben na ranar Asabar da ta gabata.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Atiku da Obi sun ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, inda suka sha alwashin dawo da huruminsu a kotu .

‘Yan takarar biyu sun yi fatali da matakin sasantawa da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi, wanda a jawabinsa na amincewa da shi bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Laraba, ya bukaci su mara masa baya a kan aikin gina kasa.

Atiku da Obi sun yi magana ne a taron manema labarai daban-daban a Abuja ranar Alhamis.

Don ci gaba da tattaunawa, dukkan ‘yan takarar shugaban kasa sun bukaci PEC a Abuja da ta ba su damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaben na ranar 25 ga Fabrairu.

Bukatar tasu na kunshe ne a cikin wasu tsaffin kudirori guda biyu da suka shigar a sakatariyar PEC da ke kotun daukaka kara a Abuja.

Dukkan kudurori biyun, tare da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa da wasu mutane biyu a matsayin wadanda ake kara, an jera su domin sauraren karar ranar Juma’a (yau).

Daga Fatima Abubakar.