Mukaddashin babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamba, ya fara rangadin aiki a jihar Sokoto a yankin na 8 Division of Responsibility.a
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar.
Da ya isa Sokoto da sanyin safiyar ranar, Mukaddashin COAS ya zarce zuwa sansanin Operation Base Tangaza da Bataliya ta 248 a Illela, inda ya samu bayanai kan yanayin tsaro daga babban hafsan runduna ta 8, Birgediya Janar Ibikunle Ajose.
Da yake jawabi ga sojojin da aka tura a Tangaza da Illela, Janar Oluyede ya yabawa sojojin bisa sadaukarwa da jajircewarsu wajen yaki da ta’addanci da tada kayar baya a shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan.
Ya bayyana cewa ya je rangadin aiki ne domin samun bayanai na kai tsaye da kuma tantance yanayin tsaro da kalubalen da sojojin ke fuskanta.
Shugaban sojojin ya basu tabbacin basu cikakken goyon baya da kwarin guiwar sa wajen dakile ayyukan yan ta’adda da masu tayar da kayar baya a yankunan da suke da alhakinsu da kuma shiyyar Arewa maso yamma baki daya.
Ya kuma bukaci sojojin da su yi watsi da duk wani nau’i na rashin jin dadi da ka iya kawo cikas ga ayyukan da ake gudanarwa domin shawo kan kalubalen tsaro da ke addabar yankin.
Mukaddashin COAS, yayin da yake zantawa da shugaban karamar hukumar Tangaza, Bashir Salihu, sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a Illela, sun bukaci hadin kai da hadin gwiwa da sojojin.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su tallafa wa sojojin da sahihan bayanai, inda ya ce tare da goyon bayansu ne sojojin za su kare su yadda ya kamata tare da tabbatar da tsaron kasa baki daya.
Daga Fatima Abubakar.