BASHIN NAIRA BILIYAN 10:FCTA ZA TA RUFE OFISOSHIN GWAMNATI,MASU ZAMAN KANSU DA OTEL-OTEL.

0
64

Yayin da ma’aikata ke shirin komawa bakin aiki bayan hutun Ista, wasu ofisoshin gwamnati, otal-otal, filaye da sauran wuraren kasuwanci na iya kasancewa a kulle saboda basussukan da Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB) ke bi.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin da babban sakataren dindindin na FCTA, Mista Olusade Adesola ya kafa don kwato sama da Naira biliyan goma da wasu hukumomin gwamnati da wuraren kasuwanci da gidajen zama a babban birnin kasa wayan da ake bin bashi.
Wannan bayanin ya fito ne daga Daraktan AEPB, Engr. Osilama Briamah yayin da yake jawabi ga manema labarai kan lamarin, a karshen mako.
Daraktan ya ce, kwamitin da zai jagoranta, ya ba su damar yin amfani da dukkan hanyoyin da doka ta tanada domin kwato makudan kudade daga hannun masu bin bashi, ya kuma ce basussukan da suka taru na tsawon lokaci sakamakon gaza biyan basusukan wadanda abin ya shafa.
A cewarsa, “dukkanmu muna sha’awar zama da yin aiki a cikin birni mai daraja ta duniya idan aka kwatanta da sauran kyawawan biranen duniya. Amma za mu iya yin hakan cikin nasara ne kawai idan muka kasance masu biyan haƙƙin ƙasa ta hanyar biyan kuɗaɗen kayan aikin mu musamman na tara datti da ruwa”.
“Abin takaici, hukumomi da yawa, gidajen zama, otal-otal, filaye da sauran su, ba sa biyan kudadensu kamar yadda ake tsammani. Hakan ya sa da wuya a samu kudaden da ake bukata don gudanar da babban birni kamar Abuja.”
Ya ce, daga karfe 5:30 na safiyar ranar Talata 19 ga watan Afrilu, bisa ga umarnin kotu da hukumar AEPB ta riga ta samu, kwamitin zai fara aikin rufe wadannan kayyakin da nufin kwato makudan kudaden da ake bin su.
Ya koka da yadda hukumar ta AEPB ta yi yunƙurin samar da hanyoyin saukaka wa masu bin bashin ta hanyar sasantawa amma abin ya ci tura, ya ce abin da ya rage shi ne a yi amfani da hanyoyin da doka ta tanada ta hanyar aiwatar da umarnin kotu na rufe wuraren da abin ya shafa.
Daraktan, ya ce masu bin bashin da abin ya shafa za su iya guje wa abin kunyar da ke tafe ta hanyar tabbatar da biyan bashin da ake bin su cikin gaggawa.
Ya bayyana cewa za a iya biyan kuɗin cikin sauƙi ta hanyar tashar Remita.

Daga Fatima Abubakar