Bayyanai game da lalluran chemerism

0
53

Ko kunsan cewa akwai wata cuta da ake kira da chimerism a turance?
Wannan Chimerism din cuta ce ko kuma ince larura ce da ba a cika samun ta sosai ba. Kashi 10% cikin 100 ke da cutan ana gane wannan cutan ne ta hanyan gwajin jini. Masu cutan nan ana samun su da kwayar jinin halitta guda 2 wato blood types a turance
Chimerism ya rabu kashi 3
1 attractive chimerism
2. Tetragametic Chimerism/ chimera
3. Twin chimera

1.Artificial chimerism kuma yana samuwa a yayin da aka yiwa mutum karin jini, stem cell transplant ko kuma bone marrow transplant. Daga wani yana dibar kwayar halittar wanda aka diba nashi zuwa wanda aka yi wa karin

2.Tetragametic Chimerism Kuma yana samuwa ne yayin da kwayoyin halitta biyu suka zama daya sannan suka shiga cikin human embryo da kwayar halitta da ya hadu

3.Twin Chimerism ana samun shi ne yayin da ake da cikin yan biyu sai wani ya mutu a ciki dayan zai ja kwayar halittar dayan sannan nashi ya canza ko kuma yazama yana da kwayar halitta biyu.

Alamomin Chimerism
Alamomin wannan larura na da yawa amma ga kadan daga ciki

1. Ido kala biyu abunda ake nufi anan shi ne kwayar idon mutum yazama kala biyu misali brown da blue

2. Gwajin jini wata DNA kala biyu

3 hyperpigmentation watau duhu a fatar mutum kokuma hypopigmentation watau karin haske a fatar mutum

Daga: Fatima Muhammad Babamallam