Bikin budar Kai na Ango Salam tare da Amaryarsa Hadiza

0
14

Budar Kai Wata Al ada CE ta masarauta , haka yake a masarautar Gombe . A ranar 21 ga watan Junairu 2024 aka gudanar da gagarumin bikin budar Kai na Dan gidan Sarkin dajin Gombe wato Salim

Anfara bikin NE da nadin Ango bayan gabatar da jawabin godiya daga Bakin Muhammad Suraj wato Galadima inda bayyana cewa wannan nauyine daya rataya akansa kuma yaji dadin da wannan biki sannan yana yiwa al ummar masarauta da wadanda suka halarci bikin godiya,

Daga Nan sai sardaunar dawaki kuma Dan mori ya fara Nadin . Anyi Nadin ne da fari da Jan yadi kamar yadda Al adar masarauta take wato Nadin sarautar chiroma

Daga Nan sai aka fara gabatar da budar Kai inda Amarya ta taho tare da rakiya kawaye ta  suka fito, suma dangin Ango suka gabato  don gudanar da budar Kai. Bayan tirka- tirka kamar yadda Al adar kawayen Amaryar keyi sai Hajia Maimuna Yaya Abubakar ta fito ta raba tirjiya. Daga Nan sai aka shiga Budar Kai gadan gadan.

Kasance da shirin biki bidiri na wannan makon a gidan Talabijin na Tozali kan lambobi kamar

Dstv: 393

Startimes: 183

GOTV: 18

Canal plus: 288