Ya kamata yawan al’umman arewa yayi tasiri wajen samun romon damokuradiyya – Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe.

0
8

Ya kamata yawan al’umman arewa yayi tasiri wajen samun romon damokuradiyya – Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe

Gyara kayanka

Babban daraktan gudanarwa na kungiyar Dattawan Arewa Ferfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe ne ya shaida hankan a wani zantawa na musamman cikin shirin Gyara Kayan ka na gidan talabijin din Tozali.

Inda ya kuma bayyana cewa al’ummar arewa basu lamunci yunkurin da ake na maida wasu manyan hukumomin gwamnati Jihar Legas ba, saboda Abuja ne cibiyar gwamnatin kasa.

 

Yace “maida wasu manyan bangarorin babban bankin kasa CBN da kuma maida hukumar kula da harkan sifurin giragen sama na kasa FAAN bai dace ba.

Ya Kara da céwa “Wannan wani mummunan zagon kasa ne ga yankin arewa.”

 

Akan batun matsalan rashin tsaro da ya addabi yankin arewa kuma Farfesa Sadiq Gombe yace hakan ya samo asali ne daga baragurbin shuwagabanni da manyan ‘yan siyasa dake wakiltan arewa a majalisan dokokin tarayya , wanda hakan yasa basa iya kawowa yankin su cigaba.

 

Farfesa Sadiq Gombe ya kara da cewan lokaci yayi da jama’an arewa zasu bar adawa maras kan gado su koma zaban shuwagabannin bisa cancanta,don cigaban yankin.

Ata bakin sa “Babban matsalar mu shine rashin zaban shuwagabannin da zasu bamu wakilci mai inganci.

Matukar bazamu hada kai musanya kishin yankin a gaba ba to muna cikin matsala.”

Haka zalika yace “A damokradiyya yawan Al’umma yana da matukar tasiri don haka babu dalilin da zai sa mutanan arewa baza su gani a kasa ba “

Farfesa Gombe ya kuma kara nuna takaici kan yadda sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya suke ko in kula da lamuran al’umma saidai maida hankali kan abunda zaije aljihun su,misali motocin da za’a saya musu na miliyan 160 kowani mutum ya saya.

Farfesa Sadiq ya kuma jaddada cewan lokaci yayi da matasa da dattawan arewa su fara fafutukar hana duk wani koma baya a yankunan su,yace “koda dai yanzu lokacine na matasa. kuma suna kira a garesu da su farka daga barci.

Daga karshe Farfesa Gombe ya bayyana raayinsu na Dattawan Arewa na rashin goyan bayan duk wani kadara daza a dauke daga Arewacin a maidashi kudanci.

 

Domin Kallo da sauraren cikakkiyar tattaunawar tasu kasance da Shirin Gyara kayanka na Tashar Tozali akan Lambobi kamar haka:

 

DSTV: 393

 

STARTIMES: 183

 

GOTV: 18

 

CANAL PLUS: 288.

Hafsat Ibrahim