Bikin Sallah:FCTA ta raba kayan abinci ga marasa karfi.

0
154

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta bayar da tallafin buhunan shinkafa 60, katun man kayan lambu 60 da kuma shanu ga talakawa da marasa galihu a fadin kungiyoyin jin kai na FCT 12 na bikin Eid-el-Fitr na shekarar 2022.

Da yake gabatar da kayayyakin abincin ga wakilan kungiyar a ranar Juma’a, Daraktan sashen kula da ayyukan babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Sani Daura, ya ce wannan babban abu na daya daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi wajen taimaka wa marasa galihu a lokutan bukukuwa.

Ya bayyana cewa, Ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Bello, yana da tsayuwar daka wajen kai wa marasa galihu.kayan abinci domin gudanar da bukukuwan Sallah da Easter da kuma Kirsimeti wanda zai sanya murmushi a fuskokinsu.

Daura, wanda ya samu wakilcin shugaban gudanarwa na sashin ka’idoji, Terfa Agor, ya bayyana cewa kungiyoyin jin dadin jama’a 12 sun hada da makarantar FCT ta makafi, Jabi, makarantar FCT na yara masu bukata ta musamman, Kuie, makarantar kurame ta FCT, Kuje, Abuja. Gidan Yara, Karu, FCT Unity Children’s Home, Gwako.

Sauran sun hada da Cibiyar Gyaran Sana’a ta FCT, Bwari, Cibiyar Gyaran Sana’a ta Al’umma, tsohuwar Karu, FCT para soccer Team, Area 10, Garki, Lepers Colony Yangoji, Cibiyar Gyaran Al’umma, Zuba, Karon-Majiji Nakasassu da Makafi Karonmajiji.

Ya yi bayanin cewa, kowacce daga cikin kungiyoyin jin kai na babban birnin tarayya Abuja sun ba su buhunan shinkafa guda biyar da man kayan lambu cartoon biyar da kuma saniya daya kowacce.

Daura ya ce: “Hukumar babban birnin tarayya Abuja a halin yanzu da Malam Muhammad Bello ke jagoranta a matsayin minista na da tsayuwar daka wajen kai wa marasa galihu a lokutan bukukuwa kamar bukukuwan Sallah da Easter da kuma bukukuwan Kirsimeti.

“Saboda haka, na bana ba wani abu ne da ya kebanta da shi ba. Dukkanin jigon wannan gabatarwar shi ne sanya murmushi na musamman a fuskokin wadannan gungun mutane,” in ji shi.

 

Daga Fatima Abubakar