Sakon Sallah daga shugaba Muhammadu Buhari

0
98

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta gabata tare da sauran al’ummar Musulmi a filin faretin Barrack na Mambila, Abuja, domin gabatar da Sallar Eid-el-Fitr.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa shugaban na Najeriya tare da rakiyar wasu ‘yan uwa da mataimakansa sun isa wurin taron da misalin karfe 9:00 na safe.

Sauran wadanda suka halarci wurin sallar idin sun hada da wasu ‘yan majalisar zartarwa ta tarayya, shugabannin tsaro, shugabannin kungiyoyin sa-kai, da jami’an gwamnati.

Sallar raka’a biyu ta gudana ne karkashin jagorancin babban limamin barikin Muhammad Dahey-Shuwa, inda ya yi bayani kan muhimmacin azumin watan Ramadan da aka kammala

Sheikh-Shuwa, a cikin hudubarsa, ya kuma yi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, inda ya yi kira ga ‘yan kasar da su ci gaba da addu’a tare da tallafa wa jami’an tsaron kasar a yakin da suke yi da ta’addanci da munanan laifuka a fadin kasar nan.

Shugaba Buhari, wanda ya amsa tambayoyi a takaice bayan kammala taron addu’o’in, ya sanar cewa ba ya samun isashen barci kan matsalar tsaro a sassan kasar.

Sai dai ya yi alkawarin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tunkarar gungun masu aikata laifuka cikin tsauri da rashin tausayi.

A zabuka masu zuwa, shugaban ya jaddada aniyar gwamnatinsa na gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da adalci.

Shugaban ya kasance a duk tsawon lokacin azumin watan Ramadan yana bibiyar al’ummar musulmi a masallacin gidan gwamnati wajen tafsirin Alkur’ani (Tafsiri).

Buhari, wanda ya halarci atisayen na yau da kullum, ya kuma karbi  baki daga sassan kasar don liyafar sallar.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Shehu Garba, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce shugaban ya yi amfani da lokutan wajen aiwatar da kyawawan dabi’u da watan Ramadan ya tsara.

Wadannan a cewarsa, sun hada da inganta da’a da sadaukarwa, kulawa, da soyayya ga marasa galihu, inganta hadin kan kasa da tallafawa sojojin kasar a kokarinsu na kawo karshen ta’addanci da sauran laifuka a kasar.

Sallar Idin Litinin ita ce karo na farko da shugaban kasa zai gudanar a wajen fadar shugaban kasa tun bayan barkewar annobar cutar corona shekaru biyu da suka gabata.

Daga Fatima Abubakar