Daya daga cikin mata biyu masu ciki da aka yi garkuwa da su a jirgin kasa ta haihu a hannun yan ta’adda.

0
298

Daya daga cikin mata masu ciki da harin jirgin kasan Abuja zuwa kaduna ya ritsa da su a ranar 28.ga watan maris da ya gabata ta haihu a karshen mako.

Wata majiya ta ce matan ta haihu ne a hannun likitoci wa’yanda yan ta’addan su ka.zo.da su domin taimaka mata yayin haihuwar.

Majiyar ta ce har ila yau ba ta da wata masaniya akan lafiyar abinda aka haifa da kuma mai haihuwar.

Mai wakiltan iyalen wa’yanda aka yi garkuwan da su Mr Jimoh ya ce har yanzu ba wanda ya tuntube su akan halin da yan uwan  su ke ci.

Daga Fatima Abubakar