Saura kwana 28 kacal a rantsar da ciyaman na Bwari a babban birnin tarayya Abuja, Mr John Gabaya ya tsinci kan shi a tsaka mai wuya.
John wanda ya tsinci kan shi a mummunar hatsarin mota a yammacin juma’a ya sa mazauna yankin cikin rudani.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a tabbatar da mutuwar su ba, hatsarin ya afku ne a kan tsakiyar hanyar Bwari inda aka ce ciyaman din ya karye a kafafuwa duka biyu.
Idan dai za a iya tunawa, watanni 18 da suka gabata ya rasa matarsa a batse, yayin da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mahaifinsa, John Makama shekara guda da ta wuce.
- Daga Fatima Abubakar