Cututtuka 5 Da shan ruwan zai iya magance su

0
17

Ruwa abin sha ne mai cike da abubuwan ban mamaki wanda ke kashe mana  kishi da kuma taimaka muna wajan  warkewa daga cututtuka daban -daban. Ruwa yana da Amfani wajan warkar da cututtuka iri -iri waɗanda za su iya afkawa manya da ƙanana. Shan isashen ruwa  zai taimaka wajan  fitar da guba, zai kuma  rage yawan kamuwa da cuta. Ko ta wace hanya, yana da mahimmanci a sha ruwan mai kyau don gujewa kamuwa da cutar da  ruwa mara kyau ke ɗauke da

Na daya Ciwon koda

Ciwon koda na iya haifar da abubuwa iri -iri, ciki har da cutar mafitsara ko na mara. Idan kuna da cystitis  wadda E. coli ke jawowa, yakamata ku sha ruwa da yawa. Ana wanke kwayoyin cutar microscopic na mafitsara ta hanyan shan  ruwa, wanda ke taimakawa wajen yaƙar kamuwa da cutar. Yawan shan ruwa sau da yawa yana hana taruwar gishiri ko wasu dati  ginuwa a cikin fitsara, wanda ke sa masa kasala. Hydration wata hanya ce mai kyau wajan tsabtace kodan da murmurewa daga cututtukan koda a mafi yawan lokuta. Koyaya, ruwan da kuke sha bai kamata ya kasance gurɓatace ba, saboda yana iya jawo wasu matsala.

Na biyu Ciwon fungal

Daya daga cikin hanya mafi inganci don yaƙar cututtukan yisti shine amfani da ruwa. Duk da cewa akwai hanyoyi da yawa don magance cututtukan yisti, amma magani mafi inganci shine  ruwa. Yisti yana haifar da kamuwa da cuta ta hanyar cin sukari a jikin ku. Lokacin da kuke shan isasshen ruwa, ana tace sukari daga jikin ku, wanda ke rage haɗarin  kamuwa da cutar yisti a jikin ku. Don hana kamuwa da cututtukan fungal, yana da mahimmanci a sha ruwa mai tsabta, mara guba.

 

Na uku Cutar numfashi

Da yawa daga cikin mu ba za su san yadda ruwa yake da tasiri wajen magance asma da sauran cututtukan numfashi ba. Cututtukan ƙwayoyin cuta na fili na numfashi sun zama ruwan dare, musamman idan yanayi ya canza. Mutumin da ke fama da cutar numfashi na iya samun alamu kamar saurin numfashi, belching, da motsin hanji, duk rashin ruwa a jikinsu ke haifar da Duk  waɗannan  matsalolin . A irin wannan yanayi, shan ruwa yana da mahimmanci, kamar yadda cututtukan numfashi ke haifar da rashin ruwa.

 

Na hudu Hawan jini

Ruwa yana taka muhimmiyar rawa wajen magance hawan jini. Ruwa yana taimakawa wajan  kara yawan jini a jikin mutum, yana sauƙaƙa wa zuciya shigar da  jinin cikinta. Rashin ruwa yana haifar da acidification na jini, wanda ke haɓaka matakan LDL cholesterol.  shan ruwa yana tsaftace jinin ku kuma yana share cholesterol mai yawa wanda ya taru a cikin  jikin mutum.

Na biyar Ciwon kai na migriane 

Mutanen da ke fama da Ciwon kai na  migraines na iya samun fa’idodi da yawa daga shan  ruwan. Babban dalilin migraines shine rashin ruwa, wanda shine dalilin da yasa kuna buƙatar kasancewa cikin ruwa a ko da yaushe. Yakamata masu fama da ciwon kai su kula  da shan ruwa da tabbatar da isasshen ruwan sha a jikin su.

By Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here