Hanyoyi 5 da zaku sarrafa  plantain inku  don ci

0
506

 

 

Ina ma’abotan son cin plantain? Ga naku nan waɗannan su ne hanyoyi daban -daban na dafa plantain inku.

Plantain ba su da tsawon rai. Kafin ku yi kefta idonku sau biyu, ya rube.

Ana ganin plantain a matsayin abin maiƙima ga mutane kaɗan kawai saboda tsadar su. Don haka, lokacin da kuka siye su a ƙarshe, baza ku so ya ɓace ba.

Don haka, menene hanyoyin sarrafa da kuma adana plantain

  1. Soyayyen plantain

Wannan shine abin da yawancin mutane suke amfani da plantain suyi. Yawancin mutane suna son soyayyen plantain, wanda aka fi sani da dodo.

Dabara anan ita ce siyan plantain waɗanda bai gama nuna ba, ta wannan hanyar yana iya dadewa ba tare da ya ɓace ba. sai dai, kuna son soya shi gaba ɗaya.

  1. Plantain da wake

Hanya mafi sauƙi don jin daɗi plantain da kuke ɗashi shine haɗa shi da wake. Plantain da wake abinci ne mai daɗi.

 

  1. Gasashen plantain

Wannan shine abin da galibi ake kira ‘Bole’. Kuna iya yin Bole a gida idan kuna da abin gashi. Ku ci da gyada ko gasasshen kifi don more rayuwan ku.

  1. Dafaffen plantain

Ga waɗanda ke guje wa cholesterol da ke da alaƙa da soyayyen abinci, dafaffen plantain ko da yaushe zaɓi ne mafi kyau. Bugu da ƙari, lokacin da kuka lura cewa plantain ɗinku suna yin taushi koyaushe kuna iya dafa shi.

  1. Faten plantain

Tabbas, zaku iya sarrafa plantain kuyi fate da shi. Kar a manta idan ana hadda faten a  ƙara masa ganye da kayan lambu don kara masa daddi.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho