DA DUMI-DUMI: SSANU da NASU sun dakatar da yajin aikin bayan ganawa da Ministan Ilimi

0
33

A yau Asabar ne kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da kungiyar masu zaman kansu ta NASU suka dakatar da yajin aikin da suke yi bayan wata ‘yar gajeruwar ganawa da ministan ilimi, Adamu Adamu a Abuja. Ana sa ran dakatarwar za ta fara aiki daga ranar Laraba.

A cewar Ministan Ilimi, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 50 don biyan alawus-alawus ga mambobin SSANU, NASU da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho