Masu garkuwa da mutane jirgin kasa zasu iya aurar da Lois mai shekara 21 ga daya daga cikin su – inji Mamu

0
129


Rahotanni daga wasu majiya mai tushe sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun sako wasu mutane hudu da suka yi garkuwa da a cikin fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, bayan da suka shafe watanni hudu suna rike a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Tukur Mamu, mawallafin Herald na Jahar Kaduna kuma mashawarcin Malaman addinin Islama kan harkokin yada labarai, Sheikh Gumi, wanda ya janye daga sassantawar, ya tabbatar da sakin mutane 4 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su ga manema labarai a Kaduna.

Duk da haka, Tukur Mamu ya kuma bayyana cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba, za a iya aurar da Arzurfa Lois John mai shekaru 21 ga daya daga cikin ‘yan ta’addan. Ya bayyana cewa daya daga cikin kwamandojin ‘yan ta’addan ya kamu da son Lois.
Muna fata gwamnati da masu sasantawa su kara daukar matakan gaggawa don ganin an sako sauran wadanda ake garkuwa da su.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho