DA DUMI-DUMIN TA:An samu wani fashewar bomb a jahar Kogi,gabannin Ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari.

0
44

Mutane uku ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a Okene da ke karamar hukumar Okene a jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis a kewayen Oyinoyi na fadar Ebira Land a garin Okene.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan kafin isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar, domin kaddamar da wasu manya manyan ayyuka.

Rukunin Masu Biyan Kuɗi Sun Jagoranci Kotu Kamar yadda Kashi 5% na Wayoyin Wayoyin Waje ke Haɓakawa A cikin Kudirin Kudi

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an tura jami’an ‘yan sanda na sashin yaki da bama-bamai zuwa wurin da lamarin ya faru.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa fashewar ta faru ne sakamakon tiransfomar wutar lantarki da ta cika da yawa da ta tashi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutanen da ke kusa da shi, wasu kadan kuma suka jikkata.

 

Daga Fatima Abubakar.