Kamfanin jiragen sama na Emirates ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Najeriya daga ranar 1 ga Satumba, 2022. Kamfanin dillancin labaran iqna ya rawaito, a shafin sadarwa na yanar gizo a ranar Alhamis cewa, kamfanin dillacin labarai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ba za ta iya dawo da kudaden da yake samu a cikin kudaden kasashen waje daga Najeriya ba.
A watan da ya gabata, Emirates ta bukaci Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama, da ya tallafa wajen dawo da kudaden shigar ta, da suka kai dala miliyan 85. Najeriya na fuskantar matsalar musayar kudaden waje kuma hakan ya kuma shafi kudin kasan watto Naira wajan faduwa idan aka kwatanta da dala. Kamfanin jirgin ya ce dakatarwar za ta “kayyade karin asara tare da rage tasirin ayyukan sa da ke ci gaba da taru a kasuwannin Najeriya”.
“Saboda haka, Emirates ta dauki matsaya mai tsauri na dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya, daga ranar 1 ga Satumba, 2022, don takaita karin asara da tasiri kan farashin ayyukanmu da ke ci gaba da taruwa a kasuwa,” in ji kamfanin. “Muna matukar nadamar rashin jin dadin abokan cinikinmu, duk da haka, yanayin ya fi karfin mu a wannan matakin.
Za mu yi aiki don taimakawa abokan cinikin da abin ya shafa su yi wasu shirye-shiryen balaguro a duk inda zai yiwu. “Idan har a samu wani ci gaba mai kyau a cikin kwanaki masu zuwa game da toshe kudaden Emirates a Najeriya, muna ci gaba da himma don yiwa Najeriya hidima, kuma ayyukanmu na samar da hanyoyin da ake bukata ga matafiya na Najeriya, samar da damar kasuwanci da yawon bude ido zuwa Dubai, da kuma babbar hanyar sadarwar mu ta sama da wurare 130.” A watan Mayu, Kungiyar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA) ta koka kan gazawar kamfanonin jiragen sama na kasashen waje wajan dawo da kusan dalar Amurka miliyan 450 da suka samu.
Daga cikin kudaden, IATA ta ce Najeriya kadai tana rike da kusan dala miliyan 450 saboda karancin kudaden waje (FX) da kuma raguwar ajiyar kudaden. Sam Adurogboye, mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA, a wata zantawa da ya yi da TheCable, ya roki gwamnati da ta taimaka wa kamfanonin jiragen su dawo da kudaden.
Daga Firdausi Musa Dantsoho