Majalisar Wakilai ta fara bincikan Ma’aikatar Aikin Gona kan N18.6bn da ake zargin an kashe wajen gyaran daji, shirya filaye da sauransu

0
89

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da asusun gwamnati ta fara bincike kan Naira biliyan 18.6 da ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta kashe wajen shirya filaye.

Shugaban kwamitin, Oluwole Oke (PDP, Osun), ya bayyana haka ne a yayin wani taron jin ra’ayin jama’a a ranar Talata, inda ya ce an kashe kudaden ne tsakanin shekarar 2013 zuwa 2021 wajen aikin share daji, da shirya filaye, da kuma gyara dakunan gwaje-gwajen kasa da na shuki.

 

Ya bayyana cewa an fitar da kudin ne daga kuri’ar hidima ta ma’aikatar.

 

Mista Oke ya ce wakilin ma’aikatar ya bayyana gaban kwamitin amma mambobin kwamitin ba su gamsu da bayanin da ma’aikatar ta yi ba.

“Mun gayyaci ma’aikatar noma kuma sun gabatar da jawabi. Sai dai wasu daga cikin mambobinmu da ya kamata a ce mazabun da wadannan ayyuka za a yi su sun yi shakkun kasancewar wadannan ayyuka. 

“Don sauraron shari’ar gaskiya, mun gayyaci kamfanonin da suka samu kwangilar da su zo su gaya wa wannan kwamitin inda da kuma lokacin da aka aiwatar da ayyukan,” in ji Mista Oke.

Ya kara da cewa idan kamfanonin suka gaza bayyana a gaban kwamitin, ‘yan majalisar za su yi amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen tilasta musu yin hakan.

 

Mista Oke bai bayyana kamfanonin da abin ya shafa da kuma ranar da za su bayyana a gaban kwamitin ba.

Kwamitin Asusun Jama’a, wanda kwamitin tsarin mulki ne, yana da alhakin kula da rahoton babban mai binciken kudi.

Daga Firdausi Musa Dantsoho