Dan tsohon shugaban majalisar dattawa ya mutu a shekaru 51 bayan ya sha fama da cutar kansa

0
47

 

Tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark, ya tabbatar da mutuwar dansa na farko, Tunde, kuma ya bayyana yadda Biochemist in ya mutu bayan ya sha fama da cutar daji a Burtaniya (Birtaniya).

 

 Mark ya ce wanda ke horar a Havard, wanda suke sa ran zai yi nasara a yakin da yake yi da cutar, ya mutu ne bayan ciwon da ke tare da shi ya yi galaba a kansa kuma ya ja numfashin sa na karshe a kasashen waje.

 

 Ya kara da cewa kasancewan sa a raye ya kasance babbar fata ga iyalansa yayin da yake bikin cikarsa shekarun sa 51 da haihuwa sati daya bayan mutuwarsa.

 

 Tsohon dan majalisar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Paul Mumeh, ya ce  burin su  bai cika  ba.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho