Buhari ya kori shugaban hukumar NDDC, ya amince da sabon tsarin mulki

0
40

Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya kori Effiong Akwa, shugaban hukumar ci gaban yankin Neja-Delta .

A wata sanarwa da Patricia Deworitshe, daraktar yada labarai ta ma’aikatar harkokin Neja Delta ta fitar a ranar Alhamis, shugaban ya kuma bayyana kundin tsarin mulkin sabuwar tawagar gudanarwa da hukumar gudanarwa ta NDDC.

A watan Disambar 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige Kemebradikumo Pondei a matsayin mukaddashin darakta na NDDC – ya nada Akwa a matsayin shugaban hukumar.

A cewar sanarwar, za a mika sunayen sabbin kungiyar gudanarwa da hukumar gudanarwa ga majalisar dokokin kasar domin amincewa.

Masu ruwa da tsaki a yankin Neja Delta sun bukaci shugaban kasar da ya kafa kwamiti mai inganci da gudanar da hukumar domin bin doka.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho