Gwamna Inuwa Ya Ziyarci Tinubu, Inda Ya Nemi Haɗin Gwiwa Tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin Jihohi

0
18

Gwamna Inuwa Ya Ziyarci Tinubu, Inda Ya Nemi Haɗin Gwiwa Tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin Jihoh

Gwamnan Jihar Gombe Kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya CON, a safiyar jiya Alhamis ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.

Gwamnan ya yi amfani da ziyarar wajen jan hankalin shugaban na Najeriya kan abubuwan dake faruwa a jiharsa dama arewa.

Ya shaidawa Shugaban ƙasar irin nasarorin da jihar ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa a matsayinsa na Gwamna, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta ƙara ƙaimi wajen kawo ci gaba cikin sauri a jihar.

Da yake zantawa da ‘yan jarida na fadar shugaban ƙasar jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaba Tinubun, Gwamnan ya jaddada buƙatar ƙarin haɗa kai tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi wajen inganta rayuwar al’umma, inda yace yin hakan zai taimaka matuƙa wajen samar da ci gaba a dukkanin ɓangarori.

Yace: “Mun yi tattaunawa da dama a ƙarshe-ƙarshen shekarar 2023, musamman waɗanda suka shafi kiwon lafiya da bada damar sake fasalin harkokin kasuwanci da sauran su.

Matuƙar ba mu inganta tattalin arziƙi ta yadda zai kyautatu ba, za mu ci gaba da kasancewa a inda muke ko ma abubuwa su ƙara taɓarɓarewa.

“Haɗin gwiwa tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya; dama ƙananan hukumomi yana da matuƙar mahimmanci a garemu, don in ba haka ba, za mu iya sauƙe nauyin jama’a dake kanmu ba.”

Da yake tsokaci kan mahimmancin noma ga ci gaban jama’a da kuma samar isasshen abinci, Gwamnan yace akwai buƙatar manoma su rungumi dabarun noma na zamani don bunƙasa sana’arsu.

“Kamar yadda yake a yanzu, dole ne jama’a su rungumi harkokin noma na zamani. Akwai buƙatar kayan aiki da suka haɗa da injuna da na’urori, da yadda za a riƙa sarrafa su, tomi mun yi sa’a Gombe tana cikin Jihohin da suka kasance manyan cibiyoyi na aikin noma.

“Mun assasa cibiyar masana’antu inda za mu iya sarrafa duk albarkatun noma da muke da su a Jihar. Ina ganin idan dukkan Jihohi za su shiga wannan tsari kuma su yi aiki tare da gwamnatin tarayya, za mu kai Najeriya inda ake buƙata cikin sauki,” in ji shi.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma yi tsokaci kan ƙalubalen tsaron dake damun wasu sassan ƙasar nan. Sai dai ya yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubun bisa tura Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima zuwa jahohin Kaduna da Filato, don jin cikakken bayanin abinda ya faru a Tudun Biri, da ƙananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi.

“A matsayina na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, na yaba da matakin da Shugaban Ƙasa ya ɗauka don gano tushen abin da ya faru a waɗannan Jihohin biyu da kuma alkawarin da ya yi cewa za a ɗauki matakin da ya dace don hana faruwar irin hakan a nan gaba. Ina gode masa bisa tallafin da yasa aka baiwa waɗanda abin ya shafa,” in ji Gwamnan.

Da yake jawabi musamman kan rikicin Jihar Filato, Gwamnan yace akwai buƙatar a sake duba dalilai na kusa dana nesa da suka haddasa lamarin don samar da mafita mai ɗorewa.

“Duk da cewa wannan al’amari ya daɗe yana faruwa, lokaci ya yi da masu ruwa da tsaki za su zauna a teburin tattaunawa su gayawa juna gaskiya, sannan su ɗauki matakan da zasu ƙarfafa ƙaunar juna. Kafin yanzu dai, jama’armu suna zaune lafiya suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum”.

“Wasu daga cikin manyan batutuwan da ake ganin sun sa wannar matsalar ta ƙi ci ta ki cinyewa sun haɗa da rikicin manoma da makiyaya, da batun baƙi da ƴan ƙasa. Amma a duk duniya, idan kowace al’umma ko ƙasa ba zata yi maraba da baƙi ba, irin wannar al’ummar ba za ta taɓa ci gaba ba.

Bayan haka, mu anan dangi muke uwa ɗaya uba ɗaya. “Saboda haka, muna jajantawa waɗanda suka rasa ‘yan uwansu. Bai kamata a samu wani dalilin da zai sa wani ya je ya raunata ko ya kashe ɗan uwansa ba, tunda ba yaƙi ba ne. Hare-haren ramuwar gayya ba zasu kai mu ko’ina ba, don haka abin da ya kamata mu mayar da hankali a kai shi ne mu fahimci kanmu mu sani cewa muna da shugabanni a kowane mataki da za mu iya miƙa kokenmu gare su.

Gwamnan Jihar Gomben ya bada shawari da cewa “Ya kamata mu ɗabi’antu da son juna da son zaman lafiya don ci gabanmu baki ɗaya”.

 

 

Hafsat Ibrahim