Tallafin Inuwa Ya Kai Ga Ƙananan Hukumomin Ɓilliri, Kaltungo da Yamaltu Deba

0
32

Tallafin Inuwa Ya Kai Ga Ƙananan Hukumomin Ɓilliri, Kaltungo da Yamaltu Deb

Kwamitocin rabon kayan abinci a ƙananan hukumomin Ɓilliri, Kaltungo da Yamaltu Deba sun ƙaddamar da rabon kayan abincin da suka karɓa daga kwamitin rabon tallafi na Jihar Gombe ga talakawa, da marassa galihu da masu ƙaramin ƙarfi a ƙananan hukumomin.

Da suke jawabi yayin rabon, shugabannin kwamitocin Hon Muhammad Alhasan Fawu, da Dr Barnabas Malle da kuma Hon. Nasiru Muhammad Aliyu, suka ce kwamitocin sun karɓi buhunan shinkafa da katon-katon ɗin taliya, kuma tuni suka fara raba su ga waɗanda zasu amfana a gundumomi da rumfunan zaɓe.

Shuwagabannin waɗanda Kwamishinoni ne a gwamnatin jihar, suka ce mutane 25 ne za su ci gajiyar tallafi a kowace rumfar zaɓe a kananan hukumomin.

Suka ce a kowace rumfar zaɓe, an zaɓo matan da mazajensu suka rasu, da masu buƙata ta musamman, da tsofaffi da marasa galihu a matsayin waɗanda suka amfana.

A jawabansu daban-daban, shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin Yamaltu Deba Ibrahim Aliyu, dana Kaltungo Aron Andrew Labte da kuma takwararsu ta Ɓillliri Hajiya Hauwa Ibrahim, sun buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin su tuna da abokai, ƴan uwa da maƙwabta a tallafin da suka samu.

Da suke bada tabbacin yin adalci a rabon, shuwagabannin riƙon ƙananan hukumomin sun yi ƙira ga waɗanda tallafin bai kai gare su ba su ƙara haƙuri, suna masu tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba suma nasu zai iso.

A nashi jawabin, Mai Tangle Malam Ɗanladi Sanusi Maiyamba, da ɗan majalisa mai wakiltan Ɓilliri ta Gabas a Majalisar Dokokin Jihar Hon. Yakubu Daniel, sun yi ƙira ga masusau hanu da shuni da ƙungiyoyi su yi koyi da Gwamna Inuwa Yahaya, wadda suka bayyana a matsayin shugaba mai ƙauna da tausayin al’ummarsa.

A jawabansu na godiya, shugabannin Jam’iyyar APC na Ɓilliri da Kaltungo Isiaka Zakari da Ayuba Hasan, da kuma takwaransu na gundumar Gwani-Shinga-Waɗe Abdulaziz Muhammad, da wakilin ƙungiyoyin fararen fula a Yamaltu Deba Salihu Abdullahi da sauran waɗanda suka ci gajiya, sun yabawa gwamnan bisa taimakon talakawa da marasa galihu a wannan lokaci da farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanan nan ne Gwamna Inuwa ya sake ƙaddamar da wani rukunin rabon tallafin kayan abinci ga talakawa da marasa galihu, inda aƙalla mutane 90,000 zasu ci gajiya a ɗokacin gundumomin jihar 114.

 

Hafsat Ibrahim