Gwamna Inuwa Yahaya Ya Cika Da Farin Ciki Yayin Da Ƴar Jihar Gombe Ta Yi Nasara A Gasar Karatun Al-Ƙur’ani Na Duniya A Ƙasar Jordan
…Yana Mai Cewa Nasarar Haraja Abin Alfahari Ne Ga Gombe Da Najeriya
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya bayyana jin daɗinsa kan samun gagarumar nasarar da wata budurwa ƴar Gombe Hajara Ibrahim Dan’azumi ta samu a gasar karatun Alƙur’ani na mata ta duniya da aka gudanar a Ƙasar Jordan.
Hajara Ibrahim, daga makarantar Islamiyya ta Abubakar Siddiq kuma ɗalibar aji 2 a Jami’ar Jihar Gombe a tsangayar ilimin kimiyyar tsirrai (Botany) wacce ta wakilci Najeriya, ta zama zakara a tsakanin sauran ‘yan takara daga ƙasashe 39 a gasar Izu 60 tare da Tajwidi a gasar Hashimawa ta duniya karo na 18 ta mata a Jordan.
A gasar da aka gudanar tsakanin ranakun 17 zuwa 22 ga wannan wata na Fabrairun 2024, Hajara ta samu maki mai ban sha’awa 99.5 cikin ɗari, inda ta yiwa saura fintinkau, lamarin da ya kaita ga lashe gasar karo na 18 wadda Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci da Kula da Wurare Masu Tsarki na Jordan ke shiryawa duk shekara.
Da yake tsokaci kan wannar nasara, Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa saƙon taya murna ga Hajara da iyayenta da malamanta, inda ya yaba da wannan kwazo da jajircewarta ga koyon Alkur’ani, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa wannar nasarar data samu zata zama abar ƙarfafa gwiwa ga al’ummar Jihar Gombe da kewaye.
Sai ya jaddada muhimmancin riritawa da tallafawa ilimin matasa musamman a fannin karatun addini, lamarinda yace yana taka muhimmiyar rawa wajen saita halaye da tunaninsu, tare da bada gudunmawa ga ci gaban al’umma.
“Ina matuƙar alfahari da irin gagarumar nasarar da ‘yarmu ta samu a duniya. Nasarar da Hajara ta samu yana nuna ƙwarin harkokin ilimi a Jihar Gombe. Nasarar data samu ba mu kaɗai ta sanya farin ciki da alfahari ba, har ma da Najeriya baki ɗaya. Na yi imanin cewa wannar nasara za ta zaburar da wassu da dama musamman ƴan matanmu,” in ji Gwamnan.
Ya ci gaba da cewa, “Za mu ci gaba da jajircewa kan ƙoƙarinmu na bunƙasa ilimin matasa musamman a fannin karatun addini. Mun san irin gagarumar rawar da wannan fanni ke takawa wajen kyautata ɗabi’u da ci gaban al’umma. Gombe ta yi fice sosai, kuma za mu ci gaba da taimakawa masu ƙoƙarin ɗaga suna da darajar Jihar Gombe a duniya, kuma Hajara na ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane, muna alfahari da taya ta murna.” Yayin da Hajara ke kan hanyarta ta dawowa Najeriya nan da ƴan kwanaki, Gwamna Inuwa Yahaya yana fatan tarbarta a ofishinsa, yana mai cewa zuwan nata zai zama wani abin ƙarfafa gwiwa ga wassu don su bi sahunta wajen fafutukar ganin sun yi fice a fannoni daban-daban, yana mai jaddada mahimmancin nuna farin ciki da goyon baya ga nasarorin da jihar ke samu. P
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe