Gwamnan Kano Ya Maida Muhuyi Magaji A Matsayin Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

0
17

Gwamnan jihar KANO, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya amince da mayar da Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa, PCACC, domin kammala wa’adinsa.

Ku tuna cewa gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da Barr Muhyi daga aiki.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya sanyawa hannu kuma ya fitar, ta ce an dawo da aikin ne nan take tare da bin umarnin kotu.

Firdausi Musa Dantsoho