Ku Bayyana Kadarorinku Yanzu, Gwamnan Kano Ya Fadawa Kwamishinonin

0
13

Gwamnan jihar KANO, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya umurci daukacin wadanda aka nada na kwamishinoni 19 da su bi ka’idojin bayyana kadarorinsu.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya sanyawa hannu, ta wannan sanarwa, ana sa ran wadanda aka zaba za su bayyana kadarorin su cikin mafi kyawun lokaci kafin a fara tantance su a majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya sha alwashin cewa babu wani kwamishina da za a rantsar da shi a matsayin memba na majalisar ministoci ba tare da cike fom din bayyana kadarorinsa daga Ofishin Code of Conduct Bureau ba.

“Duk sauran masu rike da mukaman siyasa a karkashin wannan gwamnati su ma za su bi umarnin da aka ba su.”

Gwamna Yusuf na fatan jaddada aniyarsa ga mutanen jihar Kano nagari cewa gaskiya da rikon amana ya kasance ginshikin tsarin gwamnatinsa wanda za a yi amfani da shi wajen ganin ya jagoranci kyakkyawan shugabanci kamar yadda ya yi alkawari a tsarinsa a lokacin yakin neman zabe.

Firdausi Musa Dantsoho