Gwamnan Zamfara Yasha Alwashin Tallafawa Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Gummi.

0
13

Gwamnan Zamfara Yasha Alwashin Tallafawa Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Gummi

 

Muhammad Suleiman Yobe

Gwamna Dauda Lawal ya jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Kafin hakan dai, ruwan sama kamar da bakin kwaryar da aka yi ne a ranar Juma’a ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu yankunan karamar hukumar Gummi, inda ya lalata gidaje da dama.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar ranar Asabar, gwamnan ya nuna matukar damuwa da jajantawa wadanda ambaliyar ta shafa ta Gummi.

Sanarwar ta kara da cewa: “Na samu labari mai ban tausayi game da ambaliyar ruwa a wasu sassan karamar hukumar Gummi.

Ya ƙara da cewa “Na tuntubi hukumomin da abin ya shafa, da shugabanni, da dattawa a karamar hukumar tun bayan faruwar lamarin.

“Nan take na aika da tawaga daga gwamnatin jihar Zamfara zuwa karamar hukumar domin duba halin da ake ciki tare da bayar da agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

Ya kara da cewa “Gwamnatina ta kuduri aniyar daukar dukkan matakan da suka dace don hana afkuwar irin wannan lamari mai ciki da bakin ciki a nan gaba.

Gwamna ya kuma ƙara da cewa hannuwansa zasu kasance a buɗe domin karɓar korafi da kuma tabbatar da cewa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa sun sami tallafin da da ya dace.

 

 

Hafsat Ibrahim