Gwamnatin ta biya kungiyar ASUU cikakken albashin watan Nuwamba 2022.

0
27

Malaman da ke karkashin kungiyar malaman jami’o’i sun karbi cikakken albashi na watan Nuwamba 2022, kamar yadda aka ruwaito.

An kuma tattaro cewa bashin watanni takwas ya rage a hannun gwamnatin tarayya.

Wani jigo a kungiyar a Jami’ar Bayero Kano ya bayyana haka a wata tattaunawa da aka yi da shi a Abuja a yau Laraba.

“Wasu daga cikin mambobinmu sun fara karbar albashi kuma ina tabbatar muku da cewa mun karbi cikakken albashin mu na watan Nuwamba. Duk da haka, har yanzu ana ci gaba da rike bashin.

A ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ki biyan malaman da suka yajin aikin albashi na tsawon watanni takwas da kungiyar ta fara yajin aikin.

Malaman, a watan Oktoban 2022 kuma an biya su (rabi-rabi) a cewar Ministan Kwadago da Aiki, Chris Ngige.

Malamai a fadin kasar nan sun yi zanga-zangar nuna adawa da wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.

Ana sa ran majalisar zartaswar kungiyar ta kasa za ta gudanar da wani muhimmin taro a kwanaki masu zuwa kan batun albashin ma’aikata.

Za mu kawo muku karin bayani daga baya…

 

Daga Fatima Abubakar