GWAMNATIN TARAYYA TA DAGE DAKATAR DA TWITTER A NAJERIYA

0
49

Bayan amincewar shugaba Muhammad Buhari,gwamnatin tarayya ta dage dakatar da twitter a nijeriya.
Shugaban kwamitin fasaha na Nijeriya twitter engagement kuma darakta na hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA)malam kashifu inuwa kabir ne ya sanar da matakin.Kashifu yace an amince da hakan ne bayan wata takarda da minister sadarwa da tattalin arzikin dijital ferfesa Isa Ibrahim Ali phantami Ya rubuta wa shugaban kasa.
A cewar phantami,”Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta umurce ni da na sanar da jama’a cewa shugaban kasa muhammadu Buhari GCFR ya amince da dage dakatar da ayyukan twitter a Nijeriya daga karfe 12 na safiyar yau 13 ga watan junairu 2022.

Story By: Fatima Abubakar