Hukumar babban birnin tarayya , ta bukaci manajojin shahararren rukunin shagunan Area 1 da ke Abuja da su samar da hanyar samar da makamashi iri daya a matsayin hanyar rage gurbatar muhalli a yankin.

0
18

Sakamakon daruruwan na’urorin samar da wutar lantarki da ‘yan kasuwa ke amfani da su,Hukumar babban birnin tarayya , ta bukaci manajojin shahararren rukunin shagunan Area 1 da ke Abuja da su samar da hanyar samar da makamashi iri daya a matsayin hanyar rage gurbatar muhalli a yankin.

An dau matakin ne a karshen mako bayan da mahukuntan babban birnin tarayya Abuja da suka hada da Sashen Kula da Cigaban birnin da  Jami’an Tsaro, Hukumar Kare Muhalli ta Abuja AEPB, da Kamfanin Zuba Jari na Abuja Ltd, sun gudanar da taro da ‘yan kasuwa a kasuwar.

A cewar Hukumar, duk shagunan da aka makala da sauran gine-ginen da ba bisa ka’da  ba, da kuma wuraren ajiye motoci ba bisa ka’ida ba, wanda har izuwa yanzu za a kawar da masu ababen hawa tare da tsaftace muhallin gaba daya, tare da maido da katafaren ginin yadda yake a da.

Daraktan ci gaban  baban birnin tarayya, Muktar Galadima wanda ya bayyana haka bayan taron masu ruwa da tsaki ya ce hukumar ta FCT a halin yanzu ta yanke shawarar ganawa da manajojin kasuwar domin samun fahimtar juna kafin gudanar da aikin tsaftar muhallin.

Ya ce cunkoson da ake samu a kasuwar, tare da rashin tsaftar da ke tattare da shi, wanda hakan ya haifar da bala’i ta fuskar lafiyar jama’a da kuma lokuta na gaggawa.

“Yadda kasuwar ke cike da cunkoso da rashin tsafta ba shi da kyau ga lafiyar ‘yan kasuwa da kwastomomi,” in ji shi.

Galadima ya dage kan cewa duk masu sayar da Kebab (Suya) za su kasance a karkashin  rufi daya, yayin da za a cire wuraren ajiye motoci a cikin kasuwar, kuma “ya kamata su kasance da makamashi guda daya, maimakon sharar da kasuwar kebabbun saiti, abin da zai haifar da gurbatar hayaniya.” .

“Ya ce a matsayinmu na gwamnati, ba sai mun jira gobara ta faru ba kafin mu dauki mataki ba.

Da yake jawabi a madadin ‘yan kasuwar, Umar Uba ya godewa Hukumar FCT da ta yi tunanin cewa ya dace a gana da su domin sanar da su tsare-tsaren kawar da baragurbi a kasuwar.

Umar ya yi alkawarin cewa za su taimaka wa hukuma wajen tsaftace kasuwar tunda ita ma don amfanin su  take aiki.

 

Daga Fatima Abubakar.