Hukumar babban birnin tarayya ta kai samame a sansanonin baban bola a Abuja.

0
174

Domin magance munanan laifuka na babanbola a Abuja, hukumar babban birnin tarayya, FCTA, a ranar Talata, ta fara kwashe gidajen barkwanci, da Babanbola suka gina a Kubwa.

Tawagar Taskforce na Minister FCT, karkashin jagorancin babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da aiwatarwa ga ministan babban birnin tarayya, Ikharo Attah, da kuma shugaban tawagar tsaro ta hadin gwiwa, da CSP Solomon Adebayo suka kai samamen.

Attah a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce tawagar ta zo ne domin shawo kan matsalar tsaro a yankin, wanda ke kusa da tashar jirgin kasa ta Kubwa, inda ake kai wa mutane hari tun daga karfe 6 na yamma.

A cewar Attah “Mun zo nan ne domin mu magance matsalolin tsaro a zahiri,  da cikakken goyon baya da umarnin Ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Bello da kwamishinan ‘yan sanda Sunday Babaje domin magance matsalar ‘yan bata-gari da babanbola masu yi wa mutane barna.  mutane da dama an yi musu fashi da wuka da sauran muggan makamai tare da kwace musu kayayyakin su.

Attah ya kara da cewa ,an samu magungunan da ake sayar da su a nan, an kuma danka wa  jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA .

“Mazauna garin sun yi ta murna duk da cewa suna fargabar nuna fuskokinsu ga ‘yan jarida, sun yi matukar farin ciki saboda yawancin yaran da ke kan shingen shingen da ke kusa da nan suna yi musu fashi ba tare da fuskantar kalubale.

Dangane da dorewar, “Za mu dawo kuma za mu ci gaba da zuwa  har sai sun daina zama wannan wuri.

Wani mazaunin garin da ba ya son a ambaci sunansa saboda tsoron kada a kai masa hari ya yaba wa hukumar ta FCTA kan aikin da ta yi.

Ya ce, “Wannan wuri ne mai hadarin gaske, domin suna shan duk wani abu da zai sa su bugu,suna shan kwaya kuma suna sayar da muggan kwayoyi.kuma da zaran sun sha kwaya basa mutum ta kowa.

“Wannan abu ne mai hatsarin gaske, muna yin kasuwancinmu da rana da muke rufewa kafin karfe 6 na yamma saboda rashin tsaro a kusa da nan, mun yabawa gwamnati da ta bar mana  sana’a na gaskiya da muke yi anan.

Mark Ulogwu, wanda shi ma mazaunin yankin ne kuma wasu miyagu sun taba kai wa hari a yankin ya yi matukar farin ciki da lalata gidajen.

“Domin magance cewa ba su dawo ba gwamnati na iya sanya shinge kamar babwire ko wani abu don hana su dawowa”.

Daga Fatima Abubakar.