Ni da mata ta mun sami matsala a safiyar yau kafin mu tafi aiki. Wata ‘yar rashin fahimta ce a tsakanina da ita.

0
230

 

Ni da Mata ta duk mun yi fushi da juna.  Daga yanayin fuskata, matata ta san cewa na shirya sosai don ci gaba da rashin Magana da ita a safiyar wannan ranan.  Ita ma ta fusata bata damu da yin mun magana ba.

Na fita daga gidan sai itama ta kulle kofa ta biyo ni a baya.  Tun da ba mota muke da ba, ko da yaushe muna shiga bas ɗaya don tafiya wajan aiki kowace safiya kuma muna  tabbatar da cewa mun zaune tare da juna a  bas ɗin.

Zan sauke a Manda hill ita kuma za ta sauka a zesco.

Amma yau bana son zama kusa da ita Saboda Ina fushi da ita.  Haka na zauna a kujerar baya ita kuma ta zauna a gaba, kusa da wani kyakkyawan dan sanda .

Mutumin ya kalli mata ta.  Na ga yadda yake kallon  fuskar ta cike da sha’awa.  Sannan yace mata tayi kyau.  Mata ta ta yi murmushi ta ce masa na gode.

Ya tambayi mata ta ina za ta, sai ta ce masa za ta je aiki.

Duk wannan ina zaune a baya ina sauraron hirarsu.

“Sunana Mwansa Mweemba. Ni dan sanda ne kamar yadda kika gani a cikin kayan da nasa. An tura ni Lusaka wata guda da ya wuce. A yanzu haka ina kan hanyar zuwa wurin aiki.”

Mata ta ta gyada kai. Da conductor ya nemi mata ta ta biya kuɗin mota, jami’in ya ce zai biya, ya ciro kudi ya ce kudin motan su biyu.

Mata ta ta yi masa godiya ta yi murmushi.

Sai Dan sandan ya ci gaba da magana.

“Don haka nan ba da jimawa ba zan sauka a Munali an saukar da ni a sansanin ‘yan sanda na Chelston, ban sani ba ko za ki iya zuwa gaishe ni wata rana? Zan iya samun lambar wayarki?”

Ban ɓata lokaci ba a gurguje na taba mata ta a kafadarta nan da nan.

Ta juya.

Sai na tambaye ta.

“Da fatan kin tuna kin saka cokali a cikin akwatin abincin ranan Kasubas? Kin san kullum kina mantawa.”

Mata ta ta yi mamaki sosai.  Wata kila tana tunanin ko wacece Kasuba, me yasa na za6i magana da ita.  Kafin ta fara yin mun wasu tambayoyi na kara da cewa.

“Kiyi qoqarin ki dauke ta daga makaranta, yau zan dawo gida a makare, ki dafa min ifinkubala in na dawo zan ci abinci kafin na kwanta.”

Mata ta ta rikice.

Sannan ta kalli dan sandan ta mayar da kallonta gareni.  Ta fahimci abin da nake ƙoƙarin yi.

“Toh honey.”  Ta gyada kai.

Dan sandan ya juyo ya Kalle ni.  Ya gaishe ni.  Sai ya tambayi mata ta.

“mijinki kenan?”

Mata ta ta gyada kai.  Dan sandan ya dinga kallo na akai-akai.

Sannan ya kalleni na karshe yayi mun murmushi.

Ban yi masa murmushi.

Da muka isa Chainama na sauko daga motar, na ja mata ta tare da ni.

Mata ta ta kasa daina dariya.  Yayin da muke shirin shiga wata bas, sai ta tambaye ni.

“Honey waye Kasuba?”

“Kasuba diyar mu ce da zamu haifa nan gaba. Shiga bas mu tafi.”

Mata ta tayi dariya.

Muka shiga wata bas a wannan karon, mun zauna tare da juna ne a cikin bas in.  Kuma a wannan karon ni na biya mata kudin mota.

Lokacin da kuka bawa abokin tarayyan ku tazara, ta jiki koh zuciya,  Toh kun bar shaidan ya mamaye wannan gurbin kenan.  Ya ɗauki matsayinka ba tare da izininka ba kuma ya gina wa kansa gida a madadinka.  Kada ku bar shaidan ya sami wuri a gidanku.  Ku rufe duk wata gibi dake tsakanin ku.

Ku Sanarwa Junan ku cewa zaku  kasance tare. Ubangiji Allah ya albarkaci dukan aure.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho