Hukumar babban birnin tarayya za ta gina gidajen bahaya 10000 a yankin.

0
42

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta ce ta fara yunkurin gina bandakunan jama’a 10,000 a wurare masu muhimmanci a fadin yankin.

Daraktan hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta RUWASSA na FCT, Dakta Mohammed Dan-Hassan ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata yayin wayar da kan jama’a kan matsalolin da ke tattare da yin bayan gida.

Ya ce, a shekarar 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da dokar ta-baci kan tsaftar ruwa a kasar nan wanda ke nuni da ayyana dokar ta-baci kan yin bahaya a fili a jihohi 36 na tarayya ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Dan-Hassan ya bayyana cewa, wajen aiwatar da umarnin shugaban kasa, gina bandakunan na daya daga cikin taswirorin da za a kawo karshen bahaya a fili nan da shekarar 2025 wanda ya dace da abin da Tarayyar Turai da ma duniya baki daya.

“Akwai dokar zartarwa mai lamba 009 wadda a shekarar 2018, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar.

“Hukumar RUWASSA wacce ke da alhakin duk wadannan, tare da tallafin hukumomin bayar da tallafi da kuma abokan huldar ci gaba, za a gina bandakunan jama’a 10,000 a wurare masu mahimmanci a yankin”.

Daraktan ya bayyana cewa bandakunan za su kawo ingantuwar tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli a kowace unguwa a cikin birnin.

Ya ce kusan kashi 29 zuwa kashi 30 cikin 100 na al’ummar babban birnin tarayya Abuja na yin bahaya a fili, kuma akwai bukatar a yi katafaren ginin bandakunan jama’a domin dakile lamarin da ke barazana ga rayuwar mazauna.

Dan-Hassan ya bayyana cewa hukumar ba kawai za ta gina bandakunan ba ne, za ta tabbatar da cewa an samu sauyin hali a tsakanin mazauna yankin.

“Lokacin da kayayyakin aiki suke, ya kamata jama’a su yi amfani da su yadda ya kamata, ta hanyar kula da su. Dole ne jama’a su canza dabi’a game da bandakin jama’a bisa la’akari da mahimmancin,” in ji shi.

Daga Fatima Abubakar