Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa,ta tsara sabon jadawalin lokacin tashin jiragen kasan.

0
36

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya ta sanar da daidaita jadawalin lokacin tashi na jiragen kasa biyu na karshe daga Idu (Abuja) zuwa Rigasa (Kaduna) da kuma akasin haka.

Manajan Sashen Jirgin Kasa na Abuja-Kaduna, Mista Pascal Nnorli, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ranar Juma’a cewa an yi gyare-gyaren ne domin tabbatar da isowar jiragen kasa da wuri zuwa inda suke.

A cewar Nnorli, jiragen kasan yanzu za su tashi minti 30 kafin lokacin tashinsu na baya.

Ya ce, “’Jami’an tsaro daga Idu (Abuja) da ke tashi da karfe 3:30 na rana don isa Rigasa (Kaduna) da karfe 5:38 na yamma, yanzu za su tashi da karfe 3:00 na rana, zuwa karfe 5:08 na yamma.

Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu karancin fitowar fasinjoji kamar yadda aka saba gani kafin faruwar sace fasinjoji da aka yi a ranar 28 na watan maris din wannan shekarar 2022.

‘Yayin da jirgin ya fara aiki a ranar litinin 5 ga watan Disamba,’Yan sanda sun baza jami’ai tsaro ta ko ina a tashoshin jirgin.
Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya koma aiki
“Haka kuma jirgin KA4 na karfe 2:00 na rana daga Rigasa (Kaduna) zai tashi daga Rigasa da karfe 1:30 na rana ya isa Idu (Abuja) da karfe 3:37 na yamma maimakon 4:07 na yamma”

A cewar manajan, gyaran zai fara aiki daga ranar 12 ga watan Disamba.

Nnorli, duk da haka, ya nanata kudurin kamfanin na tabbatar da tsaron lafiyar fasinjojin sa da kaddarorinsu a cikin jiragen a kowane lokaci.

A ranar 5 ga watan Disamba ne hukumar NRC ta dawo da zirga-zirgar layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna bayan shafe sama da watanni takwas ba ya aiki.

 

Daga Fatima Abubakar.