Hukumar Kwallon Yashin Nijeriya Tayi Haɗin Gwiwa da Kamfanin Kera Motoci Na Innoson Motors

0
26

Hukumar Kwallon Yashin Nijeriya Tayi Haɗin Gwiwa da Kamfanin Kera Motoci Na Innoson Motor

Daga: Captain Yobe

Hukumar dake shirya kwallon yashi ta Najeriya (NBSL) ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da Kamfanin Ƙera motoci na Nijeriya, Innoson Motors, kamfani na farko a Najeriya dake ƙera motoci a fadin ƙasar.

Sanarwar kulla yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin aka je zagaye na biyu na gasar kwallon kwallon yashin ta ƙasa na 2024 da ake gudanarwa a birnin Nnewi, na jihar Anambra.

Anyi haɗin gwiwar domin tabbatar da kawo ci gaba da ɗabbaka wasan tun daga tushe.

Shugaban Kamfanin Innoson Motors, Cif Innocent Ifedaso Chukwuma wanda ya halarci wurin bikin buɗe gasar ya bayyana irin Son da yake yi wa wasan ya kuma tabbatar da cewa zai bada dukkanin irin gudunmawar da ake buƙata domin kawo ci gaba.

Ana sa bangaren shugaban hukumar kwallon yashi na Afrika, Mahmud Hadejia ya bayyana cewa sun yi hadin gwiwar domin tabbatar da ci gaban wasan.

 

“Haɗin gwiwar shine domin tabbatar da ci gaba wasan, tare da baiwa ƴan Nijeriya dama-Inji Hadejia.

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim