Ina Son wadda zasu gaji mulki su cigaba da Yakin Da Cin Hanci Da Rashawa  – Buhari

0
37

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna fatansa na ganin harsashin da gwamnatinsa ta kafa a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa ya dore a kasar.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da ya gana da mahukuntan kotun da’ar ma’aikata karkashin jagorancin shugabanta Danladi Umar a gidan gwamnati.

 

Ya ci gaba da cewa cin hanci da rashawa ya ci gaba da zama barazana ga kasashe, tare da sanin irin sadaukarwar da kotun da’ar ma’aikata ta kasa karkashin jagorancin shugabanta, Danladi Umar da sauran hukumomi makamantanta suka yi, a cikin tabarbarewar tattalin arziki da kuma karancin kudaden shiga.

 

“Muna fata cewa harsashin da wannan gwamnati ta kafa ya ci gaba kuma ya dore, saboda batun cin hanci da rashawa ya kasance barazana ga dukkan al’ummomi,” in ji Buhari.

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho