INEC ta kare kwangilar da ta bayar ga kamfani dake da alaka da Binani na APC

0
53

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kare kwangilar buga kayan zabe ga Kamfanin Buga takardu na Binani Printing Press Limited.

 

Ana zargin kamfanin buga takardun na da alaka da ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Aishatu Dahiru Ahmed wanda aka fi sani da Binani.

 

An tattaro cewa an bayar da kwangilar buga takardun sakamakon zabe da takardun tsaro na babban zaben.

 

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar INEC na kasa, Festus Okoye, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce an bayar da kwangilar ne bayan an tantance cikin gaskiya da adalci.

 

Okoye ya ce hukumar zaben ta gudanar da aikin tantancewa, inda ya kara da cewa ba a sanya sunan yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a matsayin daya daga cikin daraktocin kamfanin Binani Printing Press Limited ba.

 

“An ja hankalinmu kan rahoton da aka samu cewa hukumar ta ba Aishatu Dahiru Ahmed kwangilar buga wasu muhimman kayan zabe. A cikin rahoton an yi zargin cewa ta mallaki kamfanin Binani Printing Press Limited,” inji Okoye.

 

“Cinikaiyan hukumar na tafiya ne ta hanyar fafatawa a fili, kuma Binani Printing Press Limited na daya daga cikin kamfanonin da ke buga takardu na tsaro da suka nemi buga takardun tsaro ga hukumar.

 

“Bayan an duba kayan aikin kamfanin tare da gudanar da aikin da ya dace a Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci (CAC), hukumar ta gamsu da cewa su kwararrun kamfanin  buga takardu ne masu karfin fasahar da ake bukata, sanin tsaro da kwarewa wajen buga takardun tsaro.

 

“Duk da haka, ba a sanya Aishatu Dahiru Ahmed  a matsayin daya daga cikin Daraktocin Kamfanin Buga takardun na Binani.”

Daga:Firdausi Musa Dantsoho