`Yan uwana `yan Nigeria!
Ina magana ne da ku a yau cikin alhini, tare da kokarin sauke nauyin da ke wuyana cikin gaggawa, hakan na faruwa ne saboda sanin irin tashe-tashen hankula da zanga-zangar da aka yi a wasu jihohin mu ta haifar.
Wani abin takaici shine yadda aka sami tarin hazikan matasan Najeriya cikin zanga-zangar wadan da basu da wani buri ko mafarki sai na ganin an samu ci gaba mai kyau da dorewa a kasar mu.
Na ji ciwon irin asarar rayuka da aka yi a wasu jihohi, irin Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da dai sauransu, da barnata dukiyoyin jama’a a wasu jihohin, kai har ma da yadda aka rika wawushe manyan kantuna da shaguna, sabanin alkawarin da masu shirya zanga-zangar suka yi cewa, zanga-zangar za ta kasance cikin lumana a fadin kasarmu. Mu sani, rushe kadarori babu abinda zai haifar sai mayar da mu baya a matsayinmu na al’umma, domin kuwa da dan abinda muke riritawa za a sake amfani wajen sake gina abinda aka rusa.
Ina mika ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a yayin zanga-zangar. Ina so mu sani cewa, dole ne mu daina amfani da zubar da jini da tashin hankali da barna a matsayin hanyar neman biyan bukata.
A matsayina na shugaban wannan kasa, wajibi ne a kai na in tabbatar da doka da zaman lafiya. Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya dora min alhakin hakan kuma na amince, da cewa zan kare rayuka da dukiyoyin kowane dan kasa, don haka gwamnatinmu ba za ta saka ido ta bar wasu tsiraru masu boyayyiyar manufa ta siyasa su wargaza wannan kasa mai albarka ba.
A wannan yanayi da ake ciki, ina ba masu shirya wannan zanga-zangar da ma masu yinta umarni, da su dakatar da duk wata zanga-zanga, su maye gurbinta da bude kofar tattaunawa da sulhu, wanda a koda yaushe kofata a bude take ga hakan.
Najeriya na bukatar dukkan mu baki daya ne a halin yanzu, tana so mu hada kai – ba tare da la’akari da bambancin shekaru, jam’iyya, kabila, addini, ko rarrabuwar kawuna ba, mu hada kai wajen gyara makomarmu a matsayin kasa.
Ga wadanda suka yi amfani da wannan yanayi da bai dace ba don yin barazana ga kowane bangare na kasar nan, ina gargadin su da cewa: doka za ta riske ku. Sabuwar Najeriyar da muke rajin ginawa, bata tanadi wani muhalli wa kabilanci ko barazana ga wani ba.
Dimokuradiyyar mu za ta ci gaba ne kawai idan muka mutunta hakkin kowane dan Najeriya da tsarin mulki ya ba shi. Ina kira ga hukumomin tsaro da su yi amfani da hanyar da ta dace wajen ci gaba da tabbatar da doka da oda tare da bayar da cikakken tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
Kudiri na a game da kasarmu, shi ne samar da kasa mai adalci da wadata, inda kowane mutum zai ci moriyar zaman lafiya, ’yanci, da rayuwa mai ma’ana da shugabanci na-gari, bisa turbar gaskiya da rikon amanar al’ummar Najeriya. kuma ta hanyar dimokuradiyya ne kadai za a iya samar da hakan.
Shekaru da dama, tattalin arzikinmu ya kasance mai rauni kuma ya shiga tsaka mai wuya sakamakon rikon sakainar kashin da ya fuskatan wanda ya dakushe ci gabanmu. A shekara guda da ta wuce ne muka tabbatar cewa kasarmu kuma abar kaunar mu Najeriya ta kai matsayin da ba za mu iya ci gaba da yin amfani da hanyoyin magance matsaloli na wucin-gadi ba, domin magance matsalolin da suka dade suna ci mana tuwo a kwarya da kokarin ceton goben mu da ta zuriyarmu da ba a haifa ba, na tsinci kaina a wanda ba shi da zabin da ya wuce na ya dauki matakin da ya dace duk da radadinsa, don haka na cire tallafin man fetur da kuma kawar da tsarin musayar kudaden waje da yawa wadanda suka haifar da tsaiko da cikas ga tsarin tattalin arzikin kasarmu da ci gabanta da namu.
Wadannan matakai da na dauka sun toshe duk wata ribar da ’yan fasa-kwauri da masu yi wa kasarmu zagon kasa suke samu. Haka kuma sun toshe tallafin da muka bai wa kasashen da ke makwabtaka da mu na a-sai-da-rai-a-nemo-suna, da tuni kafin mu farga sun mayar da tattalin arzikinmu kashin-baya.
Waɗannan matakai da na dauka sun zama dole ne muddin muna son mu sauya wa tattalin arzikin mu sheka daga maras amfanar mu zuwa mai mana amfani. Ee! Na yarda, hakan zai haifar min da kalubale. Amma ina tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin kalubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Najeriya.
A cikin watanni 14 da suka gabata, gwamnatinmu ta samu gagarumar nasara wajen sake gina ginshikin tattalin arzikinmu da zai ciyar da yau da goben mu gaba cikin wadata. Misali, a bangaren kudaden-shiga kadai, jimillar kudaden shiga na gwamnati ya rubanya ninki biyu, inda ya kai sama da Naira tiriliyan 9.1 a rabin farkon shekarar 2024 idan aka kwatanta da rabin farkon shekarar 2023, wannan, ya biyo bayan kokarin da muke yi na toshe duk wata kafa da dukiyar Najeriya ke bi take zurarewa, da bullo da dabarun sarrafa albarkatu, da tattara kudade ta hanyar kirkire-kirkire ba tare da an dora wa mutane nauyin hakan ba.
Sannu a hankali, yawan aiki yana ƙaruwa tare da samar da wasu hanyoyin fitar da wasu albarkatun da ba man fetur ba, mun kara habaka hanyoyin cin gajiyar sabbin dammamaki da sabon yanayin tattalin arzikinmu ke samarwa.
‘Yan uwana maza da mata, tafiya fa ta soma nisa!. Mun baro lokacin da kasarmu ke kashe kaso 97% na duk kudaden shigar da take samu wajen biyan bashi; mun iso inda a yanzu kashi 68% ne ke tafiya a biyan bashi, wannan nasarar an same ta ne cikin watanni 13 kacal! Mun biya haƙƙoƙin musanyar kudade na ƙasashen waje da suka daskare a kan tattalin arzikinmu na kusan dala biliyan 5 ba tare da hakan ta kawo tsaiko a tsare-tsarenmu ba.
Wannan ya ba mu ƙarin ƴancin iya sarrafa kuɗaɗenmu ta inda a yanzu zamu kashe ƙarin kuɗi a kan ku ƴan ƙasarmu, musamman a fannin tallafa wa mahimman ayyukan zamantakewa, kamar ilimi da kiwon lafiya. Kazalika hakan ya sa Jihohinku da Kananan Hukumomin ku sun sami mafi girman kason kudi da ba a taɓa samun irinsa a tarihin ƙasarmu daga Asusun Tarayya ba.
Mun kuma kaddamar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a fadin kasar nan. Kuma muna ci gaba da kammala ayyukan da muka gada da ke da mahimmanci ga ci gaban tattalin arzikinmu, wadanda suka hada da samar da manyan hanyoyi, gadoji, layin dogo, wutar lantarki, da matatun mai da iskar gas.
Idan muka duba ayyukan babbar hanyar Legas zuwa Calabar da babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry zamu ga cewa za su bude wa jihohi 16 hanyoyin huldar ci gaban tattalin arzikin junansu, da samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki ta hanyar kasuwanci, yawon bude ido da musayar al’adu.
Masana’antar man fetur da iskar gas dinmu da ke durkushewa a baya ta kama hanyar sake farfadowa sakamakon sauye-sauyen da na sanar a watan Mayun 2024 don magance gibin da ke cikin dokar masana’antar man fetur.
A watan da ya gabata, mun kara yawan man da muke hakowa zuwa ganga miliyan 1.61 a kowace rana, kuma kadarorinmu na iskar gas na samun kulawar da ya kamata. Masu saka hannun jari suna dawowa, tuni muka shaida Sanya hannun jari kai tsaye daga kasashen waje har guda biyu na sama da dala milyan 500, duk a cikin wannan karamin lokacin.
Yaku `yan Najeriya, kada mu manta mu fa masu arzikin Gas ne da na man fetur, amma sai muka dogara akan man fetur kadai, muka manta da tarin ci gaban tattalin arzikin da ke dibge a cikin harkar makamashin Iskar Gas, muka kuma shiga facaka da kadarorin kudin kasar da sunan biyan tallafin da za mu iya samar da abinda ake tallafawa a cikin gida, domin magance wannan matsalar, nan da nan muka ƙaddamar da shirin mu na CNG don canza jigilar motocinmu zuwa amfani da iskar gas na cikin gida.
Hakan shiri ne na ceton sama da Naira Tiriliyan 2 duk wata da kasarmu ke kashewa wajen shigo da tattacen mai da dizil inda za mu zuba wadannan kudade a wuraren da za su amfanar da ‘yan Najeriya.
Domin kawo karshen wannan badakala mun shirya tsaf don raba kayyakin sufuri miliyan guda a kan kudi mai rahusa da babu tsada ga motocin `yan kasuwa masu jigilar mutane da kayayyki, wadannan kayayyaki a halin yanzu sune ke cinye kashi 80% na kudaden da ake kashewa wajen shigo da tataccen man fetur da dizil.
Gwamnatinmu ta fara rarrabawa da kafa cibiyoyin juya ababen hawa daga masu amfani da mai zuwa iskar gas a fadin kasar nan, tare da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu. Mun yi imanin cewa wannan shirin na CNG zai rage farashin sufuri da kusan kashi 60 cikin 100 kuma zai taimaka a kokarinmu na dakile hauhawar farashin kayayyaki.
Gwamnatinmu ta bai wa matasa kulawa ta hanyar kafa tsarin rance ga dalibai mai suna NELFUND. Yanzu haka an saki kudi da ya kai Naira biliyan 45.6 ga dalibai da cibiyoyinsu daban-daban, kuma ina kira tare da karfafa gwiwa ga ƙwararrun matasanmu da su yi amfani da damarsu wajen cin gajiyar shirin.
Agefe daya, mun kafa hukumar bayar da Lamuni ga masu bukata da aka zuba wa kimanin Naira Biliyan 200, duk don taimaka wa ‘yan Najeriya su samu muhimman kayayyaki ba tare da bukatar biyan kudi nan take ba, wanda hakan ya kawo sauki ga miliyoyin mutane su mallaki ababen da ba za su iya mallaka nan take ba.
Mun yi hakan ne don rage cin hanci da rashawa da kuma rage musayar kudin takarda. Ko a satin nan, na sake bayar da umarnin a saki karin kudi har Naira biliyan 50 ga hukumar NELFUND da Credit Corp daga cikin kudaden da EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati don bai wa matasa Karin lamuni.
Bugu da ƙari, mun sami zunzurutun kudi har $620 miliyan a ƙarƙashin shirin Digital and Creative Enterprises (IDICE) don ƙarfafa matasanmu, ta hanyar samar da miliyoyin aiyukan fasaha da za su sa basu damar zama zakarun gwajin dafi a duniya.
Wadannan tsare-tsaren sun hada da shirye-shiryen yaye matasa Million 3 a bangaren fasaha da ake kira 3MTT, wanda abin takaici kuma abin kunya an lalata da kuma kone daya daga cikin cibiyo\yin wannan shiri a jahar Kano a lokacin zanga-zangar.
Baya da wadannan akwai kuma Shirin Gwarazan-Ƙwararru mai taken (SUPA); da Cibiyar Nazarin Matasa ta Najeriya (NIYA); ga kuma Shirin Zakulo Hazikan Matasa (NATEP), da dai sauransu da duk muka tanada wa `yan Najeriya.
Har ila yau, mun saki sama da Naira biliyan 570 ga jihohi 36 domin fadada shirye-shiryen su na tallafa wa rayuwar al`ummomin jihohinsu, yayin da kananan ‘yan kasuwa 600,000 suka ci gajiyar tallafinmu, ana sa ran ƙarin ƙarin kananan `yan kasuwa 400,000 su ma za su amfana.
Bugu da kari kuma, Mun ware lamuni na kimanin Naira milyan daya ga kowanne mutum daya daga masu kananan sana`o`i har 75,000 da za a fara rabawa daga wannan watan.
Kana a cikin shekarar da ta gabata mun kirkiri kananan sana`o`I har guda dubu 250, kuma akwai Karin manyan cibiyoyin koyar da sana`oi har guda biyar da zamu bude nan da wata Aktoba
Akwai kuma Naira Bilyan daya da aka ware ga manyan masana’antun a karkashin lamunin mu mai kudin ruwa sau daya, don bunkasa yawan masana’antu a kasar nan da zai kawo ci gaba.
A makon da ya gabata ne na sanya hannu kan mafi karancin albashi, wanda ya Sanya a yanzu karamin ma`aikaci a Najeriya zai rika karban mafi karancin albashi na akalla N70,000 duk wata.
Watanni shida da suka gabata a Karsana, Abuja, na kaddamar da kashi na farko na shirin mu na gina gidaje a birnin Renewed Hope City and Estate. Wannan aikin shi ne kashi na farko a irinsa guda shida da muka tsara zamu gudanar a fadin shiyyoyin shida na kasar nan. Kowane ɗaya daga waɗannan biranen zai ƙunshi a kalla rukunin gidaje 1,000, ita kuwa Karsana za a samar da rukunin gidaje kimanin 3,212.
Baya ga wadannan ayyuka na gine-gine, mun kuma kaddamar da sabbin rukunan gidaje na Renewed Hope Estates a kowace jiha, kowanne rukuni ya ƙunshi gidaje 500. Manufarmu ita ce mu kammala jimillar rukunin gidaje 100,000 a cikin shekaru uku masu zuwa.
Wannan yunƙurin bai tsaya ga samar da gidaje kawai ba, har ma da samar da dubban ayyukan yi a faɗin ƙasar a yayin aikin gine-ginen kamar yadda zai habaka tattalin arzikinmu.
A bangaren Noma, muna bayar da kwarin tallafi ga manoma don kara samar da abinci a farashi mai sauki. Sannan na ba da umarnin cire haraji da ma sauran nau`ikan cajis da ake karba akan ayayyakin abinci da magunguna da suka hada da shinkafa, alkama, masara, dawa, magunguna, da sauran kayayyakin hada magungunan har na tsawon watanni 6 masu zuwa, a matakin farko na kokarin rage farashin abinci da magunguna.
A kowane lokaci ina kan tuntubar Gwamnoninmu da manyan Ministoci don hanzarta samar da abinci ga al`umma, kamar yadda muka hanzarta raba buhunhunan taki ga manoma.
Manufarmu ita ce mu noma cimaka fiye da hekta miliyan 10 na fili. Gwamnatin Tarayya ta dauki nauyin bayar da gudunmuwar duk wani abin da wannan Shirin zai bukata, yayin da jihohi zasu bayar da gudunmuwar filayen noma, hakan zai samar wa miliyoyin al’ummarmu aiki da kuma kara samar da abinci.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, mun kuma ba da odar sayo na’urorin noma, irin su taraktoci da nau`rar saukaka noma, da darajarsu ta kai biliyoyin Naira daga Amurka, da Belarus, da kuma Brazil. Ina tabbatar muku cewa kayan aikin suna kan hanya.
. Ya ku ‘yan Nijeriya, musamman matasanmu, na saurari amon koken ku. Na fahimci fushi da bacin ran da ya Sanya ku shiga zanga-zanga, kuma ina so in tabbatar muku cewa gwamnatinmu ta himmatu wajen saurare da magance matsalolin ‘yan kasar.
Amma kada mu bar fushi ya yi galaba akan mu ta inda za mu yi amfani da tashin hankali mu wargaza al’ummarmu. Dole ne mu hada kai don gina makoma mai nagarta, inda kowane dan Najeriya zai rayu cikin mutunci da walwala.
Aikin da ke gabanmu na bukatar taron-dangi ne, kuma ni ne ke jagorantar wannan gamayyar ma`iakatan a matsayina na shugaban ku. An gudanar da ayyuka da yawa wajen daidaita tattalin arzikinmu don haka lokaci yayi da zan mayar da hankali wajen tabbatar da cewa ribar wannan aiki ta isa ga kowane dan Najeriya kamar yadda na yi alkawari.
Gwamnatina tana aiki tukuru don ingantawa da fadada kayayyakin more rayuwa na kasa da samar da karin damammaki ga matasanmu, wanda tabbas za ku gani a kasa.
Kada ku bari wani ya baku labarin kanzon-kurege na cewa gwamnatinku ba ta damu da ku ba. Koda yake an sha yi muku alkawura a baya da ba a cika muku ba, Ina so ku sani cewa muna cikin sabuwar gwamnati ne, sabon zubi, sabon zamani na Sabunta fata. Aiki muke muku tuƙuru, kuma sakamakon aikin zai bayyana nan ba da jimawa ba ta inda kowa zai shaida kuma ya ji dandanon dadinsa.
Ku ba ni dama mu yi aiki tare don gina kyakkyawar makoma ga kanmu da kuma `ya`yanmu masu zuwa. Mu zabi kyakkyawan fata maimakon mummuna, mu zabi hadin kai maimakon rarrabuwa, mu zabi ci gaba a maimakon koma-baya.
Tattalin arzikin yana farfadowa; kada mu shake masa nunfashi. Yanzu da muka shafe shekaru 25 muna jin dadin mulkin dimokuradiyya, kada makiya dimokuradiyya su yi amfani da ku wajen tallata ajandar rusa doka da tsarin mulkin kasar nan wanda yin hakan zai mayar da mu da dimokuradiyyar mu can baya.
Ina! GABA DAI GABA DAI !
A karshe, ina kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya, da doka da oda a kasarmu, bisa la`akari da yarjejeniyoyin hakkin dan Adam da Najeriya ta sha rattba hannu a kai.
Tsaron rayuka da da lafiya da dukiyoyin dukkan ‘yan Najeriya sune abu mafi muhimmanci.
Na gode da kulawar ku, kuma Allah Ya c albarkaci Al’ummarmu, Amin.