Kabilar A nahiyar Afirka da ya Baiwa Mata  Damar auran Mazaje fiye da daya

0
55

Wata kabilar Fulani ta kabilar Wodaabe wacce Ke zaune a Nijar a yammacin Afirka.  Maza a cikin kabilar na tunanin cewa sunfi kowa saboda sun yi imanin cewa su ne mafi kyawun gungun maza kuma a ko da yaushe suna ɗaukar madubi a tare da su.

Auren farko na kowane namiji ko macen Wodaabe iyayensu ne suke shirya su tun suna kanana.  Wodaabe ba sa yin auren mace fiye da ɗaya,   Duk da tsattsauran ra’ayi da ke nuna cewa za a iya samun abokin aure ɗaya a lokaci guda, ba wulaƙanci ba ne ga maza da mata masu aure su sami masoya.

Mata ne ke da rinjaye a dangantaka, duk da cewa Wodaabe al’umma ce ta uba.  Watakila yana daya daga cikin ‘yan tsirarun al’ummomin Afirka da mata ke zabar mazajensu cikin ‘yanci.  Hatta matan aure suna da zabin zabar wani namiji daban da za su yi soyayya da.

Kabilar na gudanar da wani taron shekara-shekara da aka fi sani da Gerewol, inda mazaje ke yin ado, da yin kwalliya, da fafatawa a gasar kwalliya.  A yayin taron, maza suna yin ado don burge matan wasu mazan.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho