TSOHUWAR JARUMA FATI SLOW TA CE NAZIRU SARKIN WAKA YA CIRE MATA KEBURA CASA IN DA TARA A JIKINTA

0
256

Tsohuwar Yar wasan Hausa Fatima Slow ta kannywood Fati slow tace mawaki Naziru sarkin waka ya cire mata kebura casa’in da tara daga jikinta .

Ta bayyana hakanne a cikin wata hira da tayi da BBC , daga bakin mai ita. Tsohuwar jarumar ta ce asalin sunanta Fatima Uthman. An haifeta a garin Zaria, ta taso a garin kano, tayi karatu a sani mai nagge da kuma shekara. Sannan tafara Sa’adatu rimi amman bata karasa bata bari.
Ta kuma cewa ta samu wannan sunan ta Fati slow ne a wajen Marigayi Ahmad S Nuhu. Tace abin da ke sakata farin ciki a duniya shi ne intaji an ambaci manzon Allah(SAW). Wannan na sakata farin ciki sosai. Ta kara bayyana cewa ta fara film ne a dalilin taruwa da suke yi a gida da makwabta su kalli film tun tana karama take sha’awar itama ta shiga harkan film har saida ta tsinci kanta a harkan fina finan kannywood.
Ta bayyana dalilan da yasa ta fito kwanaki take ta maganganu, a cewarta, ta kwana batayi bacci ba a sanadiyar mugayen kalaman da ta jefe shi da su a cikin bidiyoyin ta datayi, domin tana tsoron ran da zata tashi a gaban Allah. Tace tayi nadama kuma shima ya yafe mata.kuma daga baya, shi ne ya zama sanadiyar taimaka mata. Ta bakinta tace, Nazir sarkin waka ne ya cire mata kebura daga jikinta da yabata naira miliyan daya kyauta.
Ta kara da cewa, yanzu haka,babbar kawarta a kannywood itace Mansura Isa. ta fadi cewa tana sana’ar siyar da shaddodi, khumra da sauran kayan sakawa na mata.
Daga karshe,tace zatayi aure in Allah ya nufa. Aure lokaci ne kuma in Allah yasa lokacin aurenta yayi dole ne tayi shi,,kuma in bai nufa ba, babu wanda ya isa ya saka ranar aurenta, sai Allah
Daga Maryam Idris