Hanyoyin da zamubi wajen koyarda yaranmu karatu tun a gida.

0
276

Koyar da yara karatu babban aiki ne sosai a garemu wanda zamu iya amfana dashi gaba a rayuwa. akwai fasaha masu ban sha’awa wanda yara zasu gano abubuwa da dama wajen koyon karatu Za su koyi karatu da fahimtar rubutun da kuma  bude ido akan haruffa, tare da iya furta kalomomi musamman idan yaro ya budi idonshi cikin karatu. Shi karatun yaro da kuma tarbiyarsa duka ana fara masa su ne tun daga farkon tasowarsa.Ba lallai dole sai yaro ya shiga makaranta zai fara karatu ba, iyaye mune zamu fara nuna masa alamun koyon karatu tun a gida kafun ma ya fara tunanin shiga makaranta wadda hakan shi zai saka kwakwalwarsa ta kara budewa,domin ya budi ido ya tashi da karatun.

Sharuɗɗa da zaabi don koyar da yaro  karatu

Da farko dai ayi kokarin kusantar dasu kusa da karatu. Ana iya yin sa tun daga ƙuruciyarsu,a yi ƙoƙari a jawo hankalinsu da littattafai cike da son sani.

Haka zalika za’a iya tanadar wa yaro dakin karatu tareda kawata masa da kayan wasa masu amfani a gareshi.

A saka wa yaro zummar son karatu kuma ana nuna masa amfaninsa a gaba.

Haka zalika za’a iya samawa yaro kayan karatu masu Magana, wadda idan yana Magana wataran shima zai iya budan baki ya fadi abunda yaji abun wasar sa tana fada.

Da zarar mun fara fahimtar ina yaranmu suka dosa wajen wasa toh mutabbata mun nuna musu yadda zasu amfana da wannan hanya ba wai muce subi zabinmu ba.

UMMU KHULTHUM ABDLKADIR