KASAR KANADA TA YABAWA WIKE SABODA KIRKIRAR SAKATARIYAR MATA.

0
10

Jakadan kasar Canada a Najeriya, Jamie Christoff, ya yabawa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, bisa samar da sakatariyar harkokin mata a babban birnin tarayya.
Jakadan ya ce irin wannan matakin ya yi daidai da yadda kasashen duniya ke gudanar da ayyukansu na inganta rayuwar mata da ‘yan mata.
Jakadan, wanda ya ziyarci Ministan domin taya shi murnar nadin da aka yi masa a matsayin ministan babban birnin kasar, ya ce kasarsa na alfahari da wasu matakai da ministan ke dauka na inganta jin dadin al’ummar yankin musamman ma mata da ‘yan mata.

Ya kuma kara jaddada aniyar kasarsa na kulla alaka a tsakaninsu, musamman a fannin noma, domin moriyar bangarorin biyu.
Tun da farko, Ministan ya bayyana aniyar gwamnatin na yin hadin gwiwa da duk wata kasa ta ketare da ke shirin kawo ci gaba a babban birnin kasar.
Ministan ya ce babban birnin tarayya Abuja na da filayen noma masu albarka kuma za ta yi maraba da duk wani hadin gwiwa da zai kai ga yin amfani da irin wannan damar domin amfanin matasa.Ya shaida wa jakadan cewa, ana samun ingantuwar harkokin tsaro a babban birnin tarayya Abuja, inda ya kara da cewa an kafa wata rundunar hadin gwiwa da za ta magance matsalar One Chance domin mutane su zauna lafiya.

Ministan ya kuma yi wa jakadan bayani kan kokarin da gwamnati ke yi na inganta kudaden shiga na cikin gida don tara kudade don ci gaba, yana mai jaddada cewa akwai bukatar daidaikun mutane da kungiyoyi su biya haraji.

Daga Fatima Abubakar.