Kotun jihar Kano ta yanke wa kaza hukuncin kisa

0
137

Wata kotun majistare da ke Gidan Murtala a jihar Kano, ta bayar da umarnin kashe wani zakara bisa zarginsa da haifar da hayaniya a unguwar. GWG.ng ta ruwaito cewa za a kashe kajin namiji, a ranar Juma’a idan ba haka ba kotu za ta ci tarar mai shi.

Kamar yadda muka samu daga Naija News Hausa, wani makwabci mai suna Yusuf Muhammad Ja’en ya koka a gaban kotu cewa kajin Isyaku Shu’aibu ya hana yan unguwar samun hutun da ya kamata kuma ya kasance cikin damunsu.
Ja’en ya yi iƙirarin cewa yawan kukan zakaran ya hana su samun kwanciyar hankali.

Alkalin kotun mai shari’a Halima Wali ta bai wa Yusuf har zuwa ranar Juma’a da ya kashe zakaran bayan ya saurari gardama daga bangarorin biyu a ranar Talata yayin da ake sauraren karar.

Rahotanni sun bayyana cewa Shu’aibu ya sanar da kotun cewa ya sayi zakaran ne domin murnar bikin good Friday kuma ya roki a ba shi izinin ci gaba da Kasancewa da shi har zuwa lokacin hutun krista kafin ya yanka shi domin bikin.

Yayin da yake la’akari da rokon da ya yi, Alkali Wali ya gargade shi da kada ya bari zakaran su yi yawo tare da bata wa mazauna yankin rai.

Alkalin kotun na Kano ya kuma bukace shi da ya tabbatar da mutuwar kajin a ranar Juma’a kamar yadda aka amince, idan ba haka ba kotu za ta ci tarar sa.

Firdausi Musa Dantsoho