Mutuwar dana ya kawo karshen rashin jituwa na da mawaki Wizkid na shekaru 12 – mawaki Davido

0
80

 

Fitaccen mawakin kasar Najeriya na Afrobeat, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa, a lokacin da ya yi fama da rashin dansa, Ifeanyi Adeleke, ya samu ta’aziyya daga babban fitaccen mawakin nan, Ibrahim Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid, wanda yake zantawa da shi ta wayar tarho kowane mako.

Da yake bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Hot FM na safe a birnin New York a ranar Asabar, Davido ya bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakaninsa da Wizkid da ta shafe shekaru 12 tana tafe, ta kare ne kwatsam a tattaunawarsu ta mako-mako.
Da yake magana a cikin faifan bidiyon, ya ce, “ni da Wiz, tsawon shekaru muna samun rashin jituwa, tsawon shekaru 12 muna rikici har kwanan nan ya yi magana kuma ina ganin abin da ya dace.

“Ina ganin canji kadan a masana’antar saboda kowa ya natsu, musamman halin da nake ciki; Mummunan yanayin da ya faru, yakan kira ni kowane mako tunda abin ya faru,” ya kara da cewa.

Ku tuna cewa Davido da matarsa, Chioma Rowland, sun rasa dansu tilo, Ifeanyi a watan Nuwamba 2022, jim kadan bayan bikin cikar sa shekaru uku.

An bayyana cewa yaron ya nutse a cikin wani tafki a gidan mahaifinsa da ke tsibirin Banana kuma an garzaya da shi asibiti a Lekki inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Firdausi Musa Dantsoho