Ku rantse ba ku saci kudin gwamnati ba, kun gina gidaje-El-Rufai ya kalubalanci tsoffin gwamnonin Kaduna.

0
10

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kalubalanci tsofaffin gwamnonin jihar da su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su sace dukiyar al’umma ba a lokacin da suke kan mulki.

 

El-Rufa’i ya fadi hakan ne a cikin hirar sa ta kafafen yada labarai na Sashen Hausa na Hukumar Yada Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).

 

Gwamnan mai barin gado ya ce daya daga cikin tsofaffin gwamnonin ya gina wani katafaren gida a kan titin Jabi, Kaduna GRA, da kudin sata.

El-Rufai ya ce, “ gwamnonin da suka shude su fuskanci al’ummar jihar Kaduna su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su taba satar asusun gwamnati ba. Zan iya rantse ban taba satar Kobo a asusun gwamnati ba.

 

“Na yi farin ciki da abin da muka gani. Ayyukan da muka fara da ingancin ayyukan, za mu kwashe shekaru muna jin dadin su,” inji shi.

 

Firdausi Musa Dantsoho