LEMUN CUCUMBER DA GANYEN NA’A NA’A

0
174

Cin danyen gurji ko kuma shan lemun sa na da amfani masu yawa  ga lafiyar jikin dan adam kamar yadda  masanan ilimin hada magunguna suka ya bayyana. Cucumber na daga cikin dangin kayan marmari daga cikin rukunin Cucurbitaceae kuma tana kunshe da ruwa mai tarin yawa. cucumber na taimakawa wajen rage rashin ruwa a jiki ballantana a lokutan zafi. 

Haka zalika shima ganyen na’a na’a yana da na sa amfanin a jikin dan adam.

Shi yasa ayau zamu koya maku yadda ake hada lemun cucumber da na’a na’a

ABUBUWAN BUKATA SU NE:

.Cucumber guda daya babba

.Sugar rabin kofi

.Kanumfari guda uku
 
.Ganyen na’a na’a
YADDA ZA,A HADA 
 
1. Dafarko Zaki tsinke ganyen na’a na’a din kada kisa iccen ganyen kawai ake bukata a wanke shi tas.
2. Sai a  yanka cucumber a  hada shi da ganyen na’a na’a  da kanumfari a  zuba a blender a nika.
3. Bayan blending sai a sa a rariyar a tace, a sa sugar a juya.
4. Sai a  matse lemon tsami  a ciki a juya.
5.  Zaki iya sa kankara ko Kuma kisa a fridge ko asha a haka idan ba’a bukatar sanyi. 
 
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here